Satifiket din bogi: An dakatar da darakta a jihar Nasarawa
An dakatar da daraktan cibiyar lafiya ta jihar Nasarawa, Samuel Atala saboda satifiket na bogi.
Shugaban hukumar kula da asibitocin (NAPHDA), Dr Mohammed Usman Adis, ya ce cibiyar ta yi biyayya ne ga majalisar jihar ta hanyar dakatar da Atala a matsayin darakta har sai an kammala bincike a kan shaidun kammala makarantarsa.
Ya sanar da hakan ne bayan gurfana da yayi a gaban kwamitin majalisar jihar Nasarawa a ranar Talata a garin Lafia.
Ya ce cibiyar ta mika takarda ga jami'ar jihar Binuwai a kan satifiket din kuma tana jiran martanin jami'ar.
Shugaban cibiyar ya ce za su ci gaba da adalci ga dukkan ma'aikatansu a bangaren karin girma don tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.
KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Shugaban NAPHDA, Dr. Adis, ya bayyana gaban kwamitin majalisar jihar bayan korafin da wani Solomon Joseph Zhekaba, ma'aikaci a cibiyar ya kai bayan ya zargi rashin adalcin da aka yi masa a bangaren karin girma.
Mai korafin ya mika kokensa gaban kwamitin a kan cewa ba a bin yadda ya dace wajen nada darakta a cibiyar.
Solomon Joseph Zhekaba ya ce,"Shine mai biye da daraktan da yayi murabus amma ya rasa dalilin da yasa ba a nada shi a matsayin da ya dace ba.
"Cewa Samuel Atala wanda ke kasansa ne aka dauka don nada shi a matsayin daraktan cibiyar duk da rashin cancantarsa."
A baya mun kawo maku cewa, wani rahoto daga jaridar Daily Sun ya bayyana cewa sakataren gwamnatin jihar Nasarawa, Alhaji Ahmed Tijjani Aliyu ya yi murabus. Sakataren gwamnatin jihar ya yi artabu da 'yan majalisar jihar Nasarawa.
Aliyu ya yi murabus ne bayan kwanaki kadan da 'yan majalisar gwamnatin jihar suka bukaci ya sauka daga kujerarsa a kan harkallar kudaden wasu ayyuka har naira miliyan 284.5 tun lokacin yana kwamishinan ilimi.
Majalisar ta bukaci ya yi murabus ne bayan tattaunawar da kwamitin ya yi a kan rahoton da aka samu.
Masu nazarin siyasa a jihar Nasarawa sun ce akwai yuwuwar sakataren gwamnatin na daga cikin masu juya mulki a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng