Rikici Ya Tsananta, Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna da Wasu Mutum Uku
- Rikicin PDP ya ƙara tsananta a jihar Ogun yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta kori Jimi Lawal da wasu jiga-jigai kan wasu dalilai
- Wani kwamiti da NWC ta kafa na ladabtarwa karkashin jagorancin Barista Odulaja ne ya ba da wannan shawarin
- Da yake martani, Jimi Lawal, tsohon hadimin gwamnan Kaduna, yace wannan wani abun dariya ne
Ogun - Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ya buɗe sabon shafi yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta kori jiga-jiganta hudu ranar Talata.
Vanguard ta ruwaito cewa kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa ya kori ɗan takarar da ya nemi tikitin gwamnan Ogun, Otunba Jimi Lawal, bisa zargin rashin ɗa'a, cin amana da yi wa kundin dokokin jam'iyya hawan kawara.
An kori Jimi Lawal daga jam'iyyar PDP ne biyo bayan karɓan shawarin da kwamitin ladabtarwa wanda NWC da NEC suka kafa karkashin jagorancin Barista Tola Odulaja.
Sauran mutum uku da PDP ta haɗa Jimi Lawal ta sallama daga inuwarta sune, Muyiwa Odebiyi, Moruf Olajide da kuma Ademola Ojoye.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jimi Lawal, tsohon hadimin gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya shiga tseren neman tikitin takarar gwamnan Ogun a zaɓen fidda gwanin PDP da ya gudana a watan Afrilu.
Da yake hira da manema labarai a Sakatariyar PDP da ke Abeokuta, shugaban kwamitin ladabtarwa, Batista Tola Odulaja, yace sun kori mutanen ne bisa tanadin Kwansutushin ɗin jam'iyya.
Odulaja yace kwamitin wanda aka kafa a watan Fabrairu, 2022 ya ba da shawarin ɗaukar matakin korar ne biyo bayan rashin biyayyar da Jimi Lawal ya nuna wa PDP ta hanyar shirya zaɓen fidda gwani.
Jimi Lawal ya maida martani
Da yake martani kan lamarin, Otunba Jimi Lawal, ya ayyana matakin korarsa da PDP ta ɗauka da, "Abun ban dariya."
Lawal, a wata sanarwa da Dataktan Kamfen ɗinsa, Austin Oniyokor, fitar, yace lamarin saba doka ne a kan wata saɓa dokar wacce a cewarsa har yanzun tana gaban babbar Kotun tarayya.
A rahotom daily Trust, Wani sashin sanarwan yace:
"An jawo hankalinmu kan cewa wai an kori ɗan takarar gwamnan Ogun a inuwar PDP, Jimi Lawal, da wasu jiga-jigai. Wannan abun dariya ne kuma saɓa doka ne kan wata saɓa dokar."
"Ta ya waɗannan mutane zasu ɗauki wannan matakin bayan lamarin na gaban babbar Kotun tarayya Abeokuta. Muna kira ga Deleget ɗinmu, jagorori, dattawa da masu ruwa da tsakin PDP su kwantar da hankulansu."
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Tona Asirin Abinda Yasa Shugaban PDP Bai Son Yin Murabus
Gwamna Wike yace hangen kuɗaɗen da PDP ka iya tarawa nan gaba ya hana Iyorchia Ayu yin murabus daga muƙaminsa.
Gwamnan jihar Ribas da wasu dake tare da shi sun ce ba gudu ba ja da baya har sai shugaban PDP ya sauka zasu mara wa Atiku baya.
Asali: Legit.ng