Ku Yafe Mun Kura-Kuran da Na Tafka a Zamanin Mulkina, Masari Ya Roki Katsinawa
- Gwamnan jihar Katsina ya roki ɗaukacin al'ummar Katsinan dikko da su yafe masa dukkanin kuskuren da ya aikata a mulkinsa
- Aminu Bello Masari, yayin kaddamar da kwamitin kamfen APC na jihar, yace akwai wasu mutane da suka nuna halin butulci
- Haka zalika Masari ya yi wasu kalaman shagube da ake ganin da tsohon SSG, Mustapha Inuwa, ya ke
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya roki mazauna jihar su yafe masa duk wani kuskure da ya yi a zamanin mulkinsa na tsawon zango biyu dake gab da karewa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Gwamna Masari ya nemi wannan afuwar ne a wurin taron ƙaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen jam'iyyar APC a jihar yau Litinin 31 ga watan Oktoba, 2022.
Vanguard tace Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wurin kira ga mambobin APC, waɗanda ke ganin an musu ba dai-dai ba da su yafe musu, inda ya ƙara da cewa sun yafe wa kowa.
Haka zalika, gwamnan ya maida martani ga wasu mutane da yake ganin sun yi wa jam'iyya All Progressive Congress da gwamnatinsa butulci sakamakon rashin cika buriknasu 100%.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalaman gwamna Masari ya nuna cewa, "Akwai wasu da suka sami 80 cikin ɗari wasu kuma kaso 70 har da waɗanda 50 suka samu amma abin mamaki suka gaza gode wa Allah."
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa duk da Masari bai ambaci suna ba amma ana ganin daga cikin mutanen da yake nufi har da tsohon sakataren gwamnatinsa, Mustapha Inuwa.
Dakta Inuwa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP bayan shan kaye a hannun Dikko Radda a zaɓen fidda ɗan takarar gwamna a inuwar APC wanda ya gudana a watan Mayu.
Na Hannun Daman Gwamnan Kwara Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
A wani labarin na daban kuma Rikici Ya Sake Kunno Kai a APC, Hadimin Gwamnan Kwara Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
Tsohon hadimin ya taka muhimmiyar rawa ba dare ba rana a tafiyar “O To Ge” da ta kai jam'iyyar APC ga nasara a zaɓen 2019.
Lamarin dai ya bude sabon shafi a siyasar jihar Kwara yayin da ake tsammanin Alhaji Musibau ka iya shiga PDP kowane lokaci.
Asali: Legit.ng