Gwamnan Gombe Ya Nada Sabbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Yi Garambawul

Gwamnan Gombe Ya Nada Sabbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Yi Garambawul

  • Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya naɗa sabbin kwamishinoni biyu da mashawarta na musamman
  • Yayin rantsar da su, gwamnan ya yi garambawul a majalisar zartaswans kana ya baiwa sabbin wuraren da zasu yi aiki
  • Ya bukaci su ji tsoron Allah yayin tafiyar da harkokin ma'aikatun da aka basu amana kuma yadda ya dace

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, a ranar Litinin ya yi wani ƙaramin garambawul a majalisa zartaswansa tare da naɗa sabbin kwamishinoni biyu da mashawarta huɗu.

Yayin rantsar da sabbin naɗe-naɗen, gwamna Yahaya yace ya ɗauki matakin ne a wani ɓangaren cika manufofin da gwamnatinsa ta sa a gaba da shugabanci nagari, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe.
Gwamnan Gombe Ya Nada Sabbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Yi Garambawul Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Gwamnan yace sabbin naɗe-naɗen sun yi daidai da kudirin gwamnatin na tafiyar da jagoranci mai kyau wanda zai cika burin da al'umma ke tsammani daga gwamnati.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici Ya Kunno a APC, Hadimin Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Inuwa Yahaya yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Waɗan nan canje canjen da muka yi game da hadimai zasu fara aiki nan take, gasu kamar haka; Dauda Batari zai tashi daga ma'aikatar Ilimi zuwa ma'aikatar ilimin gaba da Sakandire."
"Shehu Madugu daga ma'aikatar makamashi da Albarkatun ƙasa zai koma ma'aikatar muhalli da dazuka."
"Aishatu Maigari ta tashi daga ma'aikatar kimiyya da fasaha zuwa ma'aikatar Ilimi yayin da Meshak Lauco zai koma aiki a Ma'aikatar Ilimin gaba da Sakandire daga ma'aikatar yaɗa labarai da al'adu."

Wane aiki aka ba sabbin Kwamishinonin?

Bugu da ƙari, Gwamna Yahaya yace sabbin kwamishinoni Mr Sanusi Pindiga da Mr Andirya Moljengo, zasu karɓi jagorancin ma'aikatar makamashi da Albarkatu da ma'aikatar Kimiyya da Fasaha a jere.

Yahaya ya roki sabbin kwamishinonin su jajirce duba da nasarorin da gwamnatinsa ta samu kana su sa gaskiya, rikon amana yayin gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Tona Asirin Abinda Yasa Shugaban PDP Bai Son Yin Murabus

Ya bukaci su gudanar da ayyukan ma'aikatunsu da tsoron Allah kana su tabbata an yi amfani da kuɗaɗen da aka ware musu ta hanyar da ya dace, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Hadimin gwamnan Kwara ya yi murabus

A wani labarin kuma Sabon Rikici Ya Kunno a APC, Hadimin Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Hadimin gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, Alhaji Musibau Esinrogunjo, ya yi murabus daga mukaminsa.

Tsohon hadimin ya taka muhimmiyar rawa ba dare ba rana a tafiyar “O To Ge” da ta kai jam'iyyar APC ga nasara a zaɓen 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262