Dalilin Da Yasa Shugaban PDP Ya Ƙi Sauka Daga Mukaminsa, Gwamna Wike
- Gwamna Wike yace hangen kuɗaɗen da PDP ka iya tarawa nan gaba ya hana Iyorchia Ayu yin murabus daga muƙaminsa
- Gwamnan jihar Ribas da wasu dake tare da shi sun ce ba gudu ba ja da baya har sai shugaban PDP ya sauka zasu mara wa Atiku baya
- Har yanzu babu zaman lafiya a cikin jam'iyyar PDP tun bayan kammala zaɓen fidda gwani a watan Mayu
Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ba ya kaunar sauka daga mukamin ne saboda yana son cigaba da kula da kuɗaɗen jam'iyya.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Wike ya faɗi haka ne a wani taron manema labarai a Patakwal, babban birnin jihar Ribas, a ƙarshen makonnan.
Wike da makusanta sun jima suna yaƙin neman Ayu ya yi murabus sakamakon saɓawa kwansutushin ɗin da aka kafa PDP a kai wanda ya hana shugaban jam'iyya ya fito daga yanki ɗaya da ɗan takarar shugaban kasa.
Mista Ayu ya fito ne daga jihar Benuwai, arewa ta tsakiya yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya hito daga Adamawa, arewa maso gabashin Najeeiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamna Wike ya zargi Ayu da kasancewa, "Rikakƙen ɗan rashawa," kuma ba ya rike amanar kuɗaɗen da suka shiga asusun jam'iyyar PDP.
Meyasaa Ayu yaƙi sauka daga shugabancin PDP?
Da yake jawabi a Patakwal, Gwamnan jihar Ribas yace Ayu na jure matsin lambar ya yi murabus ne saboda yana son kula da manyan kudaden da PDP ka iya tarawa nan gaba.
"Meyasa ba ya son yin murabus? Yana fatan 'yan Najeriya zasu tallafa wa PDP da kuɗi don haka idan yana nan zai yi yadda ransa ke so da kuɗaɗen. Ya gama da biliyan ɗaya cikin N11bn da aka tara a zaɓukan fidda gwani."
"Kuma wannan ce jam'iyyar da baki ɗayanmu muka wa aiki domin ta kwace mulki daga jam'iyya mai mulki amma muka ce an yi ba dai-dai ba, kawai sai shugaban jam'iyya ya buɗe baki yana barazanar hana wasu takara."
"Haka ya so yi a jihar Ribas, ya zo ya mana maguɗi kuma ya ƙaƙaba wasu a takarar gwamna Amma ya sakamako ya kasance, maganinsa muka yi. Bai kamata faɗi haka ba.
- Nyesom Wike.
A wani labarin kun ji cewa Rikicin PDP Ya Kara Dagulewa, Shugaban Jam'iyyar Ya Yi Fatali da Shawarin da Dattawan mahaifarsa suka ba shi
Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya ce ba zai nemi gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai domin zaman sasanci ba.
Da yake jawabi ga dattawan mahaifarsa Jemgbah ranar Asabar, Ayu ya ce ko kaɗan babu wata matsala a tsakaninsa da Ortom.
Asali: Legit.ng