2023: Bola Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Babbar Kungiyar Yarbawa da Gwamnan PDP
Sauran shugabannin kungiyar Afenifere sun yi wa ‘dan takaran APC, Bola Ahmed Tinubu mubaya’a
Kungiyar Afenifere tana goyon bayan tsohon Gwamnan Legas ya karbi shugabancin Najeriya a 2023
Tinubu ya samu goyon bayan Reuben Fasoranti, alhali Ayo Adebanjo yana tare da Jam’iyyar LP
Ondo - Jagororin kungiyar Afenifere da gwamnonin Kudu maso yammacin Najeriya, sun nuna goyo bayansu ga takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci gidan Pa Reuben Fasoranti, dattijon da ya sauka daga shugabancin Afenifere a 2021.
A wajen wannan zama da aka yi, Reuben Fasoranti da wasu dattawan kasar Yarbawa irinsu Cif Olu Falae sun ce Tinubu ne ‘dan takararsu a zabe.
Olu Falae wanda ya yi jawabi a gaban sauran shugabannin kungiyar Afenifere na jihohin Kudu maso yamma, Kwara da Kogi sun yi wa APC mubaya’a.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyan ya nemi Tinubu ya magance matsalar tattalin arziki, ya fitar da jama’a daga talauci, ya kuma kawo zaman lafiya.
Kiran da Olu Falae ya yi
“Idan ka zama shugaban kasar nan, ka shawo kan matsalolin Najeriya. Mun zo ne domin mu bada shawara.
Ni na tsufa, na daina neman wani aiki. Muna bukatar mu magance matsalar rashin tsaro da tattalin arzikin kasa.
Mu na nan a lokacin da za kayi nasara, ka kawo shugabanci da yardar Ubangiji.
- Olu Falae
Gwamnonin Kudu sun yi na'am
The Cable tace Mataimakin gwamnan Oyo, Adebayo Lawal yace Mai gidansa, Seyi Makinde yana goyon bayan wannan zabi da shugabannin Afenifere suka yi.
Sabon Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji yace dukgwamnonin Kudu maso yamma suna tare da Tinubu. Sauran takwarorinsa sun tabbatar da haka a jawabansu.
Rahoton yace Tinubu ya samu goyon bayan Afenifere ne bayan ya ziyarci Fasoranti bayan ya samu labarin Pa Ayo Adebanjo yana goyon bayan Peter Obi a 2023.
Wannan mataki da Ayo Adebanjo ya dauka, bai yi wa manyan Yarbawa dadi ba, daga nan aka fara shirin yadda za a warware mubaya’ar da aka yi wa jam’iyyar LP.
Babu zaman lafiya a PDP
An ji labari Gwamna Nyesom Wike ya maida martani ga jawabin da aka ji shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya yi a kan hana wasu shiga takara a zabe mai zuwa.
Iyorchia Ayu ya yi ikirarin zai iya hana mutum takara, amma Wike yace Ayu bai da wannan iko, ya kalubalance shi da ya karbe tikitin 'Yan takaran PDP a Ribas.
Asali: Legit.ng