'Yan Najeriya Mazauna Waje Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Atiku, Sun Ce Ya Cancanta
- Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya samu karbuwa a idon 'yan Najeriya mazauna kasashen waje
- 'Yan Najeriya da dama sun bayyana goyon bayansu ga tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 mai zuwa
- Sun kuma bayyana bukatar a kawo hanyar da 'yan Najeriya mazauna waje za su iya zabe don kawai su zabi wanda suke kauna ya gaji Buhari
Farfesa Isa Odili ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa.
Ya kuma bayyana cewa, da yawan 'yan Najeriya mazauna kasashen waje sun nuna shawa'a da goyon bayansu ga Atiku Abubakar.
Odili, wanda shine daraktan kungiyar kamfen ta Atiku-Okowa Presidential Campaign Organisation ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng a ranar 30 ga watan Oktoba.
Jigon na PDP mazaunin kasar Kanada ya bayyana ziyarar da Atiku ya kai birnin Washington a makon jiya a matsayin ziyarar da ta dace kuma akan lokaci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma bayyana cewa, 'yan Najeriya da dama dake zaune a waje suna mararin ganin shugaban kasar da zai cire Najeriya daga kangin da take ciki, kuma sun ga hakan a tattare da Atiku.
Hakazalika, ya ce suna bukatar shugaban da yake da wayewa kuma masanin hanyar ciyar da kasa gaba.
Ya yaba ziyarar Atiku
Da yake yaba ziyarar da Atiku ya kai birnin Washington, ya bayyana cewa, wannan ziyara ce ta kan lokaci kuma, tabbas da irin wannan ziyara Atiku zai lashe zukatan 'yan kasar mazauna waje.
Hakazalika, yace Atiku ya yi ta ne a daidai lokacin da kasar Amurka ke yiwa Najeriya gargadin yiwuwar samun munanan hare-haren ta'addanci.
Ya kuma roki 'yan Najeriya da su marawa Atiku baya domin ganin an samu sauyi mai kyau kuma mai dorewa bayan zaben 2023 dake tafe nan kusa.
Hotonan Ganawar Dan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi da Sheikh Dahiru Bauchi
A wani labarin, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour na kara tsawon kafa da hannu wajen tallata kansa a fadin kasar nan gabanin zaben 2023.
Obi da abokin gaminsa, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed sun kai wata ziyara a jihar Bauchi, inda suka gana da babban malamin addini na Afrika, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Tsohon gwamnan na Anambra ya yada hotunan wannan ziyarar da ya kai ga malamin a shafinsa na Twitter a yau Juma'a 28 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng