Ba Zan Goyi Bayan Atiku Ba Matukar Ayu Ne Shugaban PDP, Gwamna Makinde

Ba Zan Goyi Bayan Atiku Ba Matukar Ayu Ne Shugaban PDP, Gwamna Makinde

  • Gwamna Seyi Makinde yace matukar shugaban PDP bai yi murabus ba, to ba zai marawa Atiku baya a 2023 ba
  • Gwamnan, wanda ke goyon bayan fafutukar tsagin Wike, yace ba gudu ba ja da baya game da bukatarsu ga PDP
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan takwaransa, Samuel Ortom na jihar Benuwai ya nemi Atiku ya ba shi hakuri

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sha alwashin ba zai goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ba matukar Iyorchia Ayu ya ci gaba da zama a kujerar shugaban jam'iyya na ƙasa.

The Nation ta ruwaito cewa Makinde ya ayyana haka ne a 'Southwest Political Circuit', wani fitaccen shirin Fresh 105.9 FM da ke Ibadan a ƙarshen makon nan.

Gwamna Makinde da Ayu.
Ba Zan Goyi Bayan Atiku Ba Matukar Ayu Ne Shugaban PDP, Gwamna Makinde Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Da yake amsa tambayar ko zai mara wa Atiku baya idan Ayu ya cigaba da zama a mukaminsa, Makinde yace zai tallata yan takarar PDP na jihar Oyo ne kaɗai a zaɓen 2023 idan har ba'a gyara ba.

Kara karanta wannan

Jigon Siyasa Ya Hango Faɗuwar Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Ɗan Takarar Da Zai Gaji Buhari a 2023

Yayin da aka tunatar da shi cewa rana ɗaya ake zaben shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya, Gwamna Makinde yace masu kaɗa kuri'a sun waye fiye da lokacin baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma jaddada cewa a yanzun mutane na zaɓen dan takarar da suke ganin ya dace ne idan buƙatar hakan ta taso.

Makinde, ɗaya daga cikin tawagar Wike da ta haɗa gwamnoni 5, yace ba gudu ba ja da baya a bukatarsu na ganin ɗan kudu ya karbi ragamar jam'iyyar PDP.

"Baki ɗaya gwamnonin kudu mun cimma matsayar ya kamata mulki ya dawo yankinmu domin zaman lafiya, adalci da daidaito. Mun nemi cewa tun da arewa ta yi shekara 8, ya kamata ɗan kudu ya karɓa."
"Mun je zaɓen fidda gwani PDP ta tsayar da ɗan arewa a matsayin ɗan takara. Tun da jam'iyyarmu ta tsaida ɗan arewa kuma muka ce a yi kaza amma aka ƙi saurarenmu sai mu tsaya a iya zaɓen jihar Oyo."

Kara karanta wannan

2023: Rikicin PDP Ya Kara Dagulewa, Shugaban Jam'iyyar Ya Yi Fatali da Shawarin Dattawa

"Ni, Seyi Makinde, idan ba'a yi abinda ya dace ba, ni ba bawa bane amma har yanzun akwai lokaci zamu ci 100 bisa ɗari a Oyo. Mutanen Oyo sun riga sun yanke hukunci saboda sun gwada gwamnatoci da dama."

- Seyi Makinde.

Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

A wani labarin kuma mun tattara muku jihohin da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a LP.ka iya yi wa Atiku Lahani a 2023

Takarar Peter Obi a zaben sabon shugaban kasa mai zuwa tana cigaba da motsa siyasar Najeriya.

Peter Obi ya samu karbuwa musamman a Kudancin Najeriya da wasu jihohi a Arewacin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262