Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023
- Gabannin babban zaben 2023, Sanata Kashim Shettima ya yi karin haske kan yiwuwar hadewarsu da dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso
- Shettima wanda shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC ya ce za su zauna su fahimci juna da tsohon gwamnan na jihar Kano a lokacin da ya dace
- Tsohon gwamnan na jihar Borno ya kuma jadadda cewa masu kokarin ganin sun raba kan kasar nan ba za su taba cimma nasara ba
Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya bayyana cewa shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata.
2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili
Tsohon gwamnan na jihar Borno wanda ke gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman birnin tarayya Abuja, yana barkwanci ne da tsohon dan majalisar wakilai, Garba Ibrahim Muhammed, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a taron.
Daily Trust ta nakalto Shettima na cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Na sha alwashin ba zan taba muzanta Sanata Rabiu Kwankwaso ba har a gama zabe mai zuwa. Shi din shugaba ne nagari, kuma da izinin Allah, za mu zauna sannan mu fahimci junanmu a lokacin da ya dace nan kusa.
“Wadanda ke shirin raba kan kasar nan ba za su cimma nasara ba, kuma saboda haka, ya zama dole mu lamunci junanmu sannan mu sadaukar da abubuwa.”
Ana Wata Ga Wata: Ma'aikatan APC Sun Barke da Zanga-Zanga Kan Hakkinsu, Sun Nemi A Binciki Adamu
A wani labarin, ma’aikatan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun koka kan cewa shugabancin jam’iyyar ya ki biyansu albashi.
Ma’aikatan jam’iyyar sun fusata ne bayan an amince da biyan alawus din gida da motoci ga mambobin kwamitin aiki duk da cewar ba a biyasu nasu albashin na watan Satumba ba har zuwa ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.
Yayin da babban sakataren APC na kasa, Felix Morka, ya yi ikirarin cewa an sasanta batun albashin ma’aikatan, ya bayyana cewa an samu tsaiko ne sakamakon wani tsari na cikin gida.
Asali: Legit.ng