Ana Wata Ga Wata: Ma'aikatan APC Sun Barke da Zanga-Zanga Kan Hakkinsu, Sun Nemi A Binciki Adamu
- An zargi shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) APC na kasa da yin babakere kan wasu kudade
- Ma’aikatan jam’iyyar wadanda suka koka kan rashin samun albashi tun watan Satumba sune suka yi wannan zargi kan shugaban nasu
- Majiyoyi cikin jam’iyyar sun yi zargin cewa Abdullahi Adamu ya amince da biyan alawus din gida da motoci ga mambobin kwamitin NWC
Abuja - Ma’aikatan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun koka kan cewa shugabancin jam’iyyar ya ki biyansu albashi.
Ma’aikatan jam’iyyar sun fusata ne bayan an amince da biyan alawus din gida da motoci ga mambobin kwamitin aiki duk da cewar ba a biyasu nasu albashin na watan Satumba ba har zuwa ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.
Yayin da babban sakataren APC na kasa, Felix Morka, ya yi ikirarin cewa an sasanta batun albashin ma’aikatan, ya bayyana cewa an samu tsaiko ne sakamakon wani tsari na cikin gida.
Bugu da kari, shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, ya sauya wasu daraktoci shida da aka dakatar a sakatariyar jam’iyyar na kasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daraktocin da abun ya shafa sune Anietie Offong (Daraktan kula da jin dadi); Bartholomew Ugwoke (Daraktan Bincike); Abubakar Suleiman (Daraktan Kudi); Dr Suleiman Abubakar (Daraktan Gudanarwa); Salisu Dambatta (Daraktan Labarai) da Dare Oketade, (Shugaban doka).
Hakazalika, akwai rahotannin da ke nuna shugaban jam’iyyar ya maye gurbin mutanen da aka sallaman da wasu, inda ya ce an yi hakan ne don tsaftace tsarin.
Da yake kare kansa, Adamu ya kuma yi watsi da zargin cewa ya mayar da hankali wajen nada hadimai da makusantansa kan wadannan mukamai da aka lissafa.
Har ila yau da suke zanga-zangar tsigesu da aka yi, wani tsohon daraktan gudanarwa na jam’iyyar, Abubakar Suleiman, ya zargi kwamitin NWC na APC karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa da kin bayyana masu laifinsu kafin aka tilasta masu tafiya hutun shekara.
Suleiman ya yi ikirarin cewa karya Adamu yayi kuma sakatariyar na a hannu mai kyau kafin ya fara aiki a matsayin shugaban jam’iyya na kasa.
Ya ce:
“A matsayinmu na daraktoci, bamu amince da komai ba. Aikinmu shine aiwatarwa. Idan jam’iyyar na ganin ba haka bane, toh a gayyaci EFCC ko sauran hukumomin yakin da rashawa don su binciki asusun APC, ciki harda na sirri wadanda shugabancin jam’iyyar ke kula da su.”
Baya ga alawus din da aka amince a biya NWC din, majiyoyi sun bayyana cewa mambobin kwamitin sun kuma biya kansu wasu hakoki na shekaru hudu.
Ya ce:
“Adamu da mambobin NWC sun biya kansu alawus din gaba. Shakka babu, suna hakan ne saboda sun san cewa da yawansu ba za su dade a sakatariyar ba kuma abun bakin ciki ne mutane da dama na tsoron magana kan haka.
“Mun tara N39bn daga siyar da fam a babban taron jam’iyyar kawai, za ku yi mamakin cewa zuwa Satumba (watan jiya), shugabancin jam’iyyar ta kashe fiye da biliyan N20 daga ciki.”
Shaidanun APC Sun Dade Da Komawa PDP, In ji Tsohon Minista
A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa shaidanun da ke cikin jam’iyyar APC duk sun koma PDP tun bayan da ya dawo jam’iyyar mai mulki a watan Satumban 2021.
Fani-Kayode wanda ya kasance mamba a kwamitin yakin neman zaben shugabancin Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV.
Ya jadadda cewa sam APCn da dana yanzu ba daya bane akwai bambanci sosai.
Asali: Legit.ng