2023: Ka Halarci Tattaunawar da Za a yi a Gidan Talabijin din Arise, Oseni ga Tinubu

2023: Ka Halarci Tattaunawar da Za a yi a Gidan Talabijin din Arise, Oseni ga Tinubu

  • Fitaccen ‘dan jarida kuma mai karbar bakunci a gidan talabijin na AriseTV ya sanar da cewa a kagauce suke su karbi bakuncin Ahmed Bola Tinubu
  • Oseni ya sanar da cewa sun karba bakuncin Obi, Sowore da wasu ‘yan takarar shugabancin kasa na a zaben 2023 don haka zasu so samun Tinubu a shirinsu
  • Yace suna son jin ra’ayoyinsa tare da shirye-shiryensa kan ‘yan Najeriya kuma su yi masa tambayoyi domin karin haske a kan hakan

‘Dan jarida kuma mai masaukin baki na gidan talabijin din Arise, Rufai Oseni, ya bayyana cewa a kagauce suke jiran ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu da Oseni
2023: Ka Halarci Tattaunawar da Za a yi a Gidan Talabijin din Arise, Oseni ga Tinubu. Hoto daga Independent.ng
Asali: UGC

Gidan talabijin din sun jiran karbarsa masayin bako domin tattaunawa da shi.

Oseni ya bayyana hakan a ranar Laraba ta shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa sauran ‘yan takarar shugabancin kasa na jam’iyyu sun halarci tattaunawa a gidan talabijin din.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Kannywood da Kyautar N50m

Ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A kagauce muke jiran ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a gidan talabijin din AriseTV
“Mun karba bakuncin Obi, Atiku, Kwankwaso, Sowore da sauransu.
“Zamu so jin nashi ra’ayoyin ga Najeriya kuma mu tattauna a kansu.”

Jama’a Sun Yi Martani Bayan Ganin Bidiyon Surkulle da Tinubu Yayi Kan El-Rufai a KadInvest

A wani labari na daban, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC yayi surkulle tare da shirme yayin da yake magana kan Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a jawabin da yayi a taron tattalin arziki da zuba hannayen jari na jihar Kaduna karo na bakwai da ya halarta.

A yayin jawabi a taron a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoban 2022, Tinubu yace Gwamnan Kaduna ya sauya:

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi

“Rubabben al’amari zuwa lalatacce. A bayyane nake rokon Gwamna El-Rufai da kada ya tafi neman karin digiri ko digirin digirgir da sauransu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel