2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

  • Takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima ta sake samun tagomashi bayan jigon APC ya mara musu baya
  • Hakan na zuwa ne yayin da tsohon ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya yi alkawarin ganin Tinubu ya ci Akwa Ibom a 2023
  • Akpabio ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya kaddamar da kungiyar kamfen a jihar gabanin babban zaben 2023

Akwa Ibom - Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya yi alkawarin tattaro kan masu zabe a Akwa Ibom da wasu wuraren don ganin nasarar dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu.

Akpabio, wanda shine dan takarar sanata na Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, ya ce tabbatar da cewa Tinubu ya zama shugaban kasa na gaba aiki ne da ya zama dole a aiwatar saboda tsaro da cigaban Najeriya, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban Yarbawa ya tona asirin Tinubu, ya fadi wata babbar illarsa da yasa ba zai zabe shi ba

BAT da Akpabio
2023: Sabon Lamari Yayin Da Akpabio Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili. Photo credit: @officialABAT @Senator_Akpabio)
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akpabio ya bayyana goyon bayansa ga takarar Tinubu, ya bada dalili

Da ya ke magana yayin kadamar da kwamitin kamfen dinsa, Akpabio ya yi kira ga dukkan mambobin APC su shiga lunguna da sakunan jihar su nemo wa Tinubu da shi da sauran yan jam'iyyar kuri'u.

Ya ce:

"Na yi shirin dawowa jihar nan ne a matsayin shugaban kasarku. Da na yi nazarin APC, na lura cewa muna bukatar zaman lafiya da hadin kai a jam'iyya tunda gwamnonin arewa sun nuna kishi sun dage mulki ya koma kudu, hakan yasa na janye takara ta na goyi bayan daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar kuma mutum mai hangen nesa da tunani, Sanata Bola Ahmed Tinubu."

Tinubu Ya Bawa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bada Naira miliyan 20 ga cocin katolika da ke jihar Benue, rahoton Legit.ng.

Rabaran Hyacinth Alia, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Benue ne ya gabatar da kyautar ta Tinubu a bikin cikar cocin shekaru 100 a Otukpo.

Wata sanarwa da hadimin Alia a bangaren watsa labarai, Isaac Uzaan ya fitar a ranar Alhamis, 27 ga watan Oktoba ta ce Tinubu yana taya fastoci, ma'aikata da dukkan mambobin cocin murnar wannan bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164