Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi da Hukuncin Korar Gwamna Umahi da Mataimakinsa

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi da Hukuncin Korar Gwamna Umahi da Mataimakinsa

  • Bayan da aka daukaka kara kan batun korar gwamna Umahi da mataimakinsa, kotu ta yanke hukunci
  • Gwamna Umahi da mataimakinsa sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ya fusata 'yan PDP
  • A baya babbar kotun tarayya ta bayyana korar gwamnan da mataimakinsa duba da wasu hujjoji da aka gabatar

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta soke hukuncin da mai shari'a Iyang Ekwo na babbar kotu ya yanke a ranar 8 ga watan Maris na koran gwamna David Umahi da mataimakinsa.

An maka gwamnan da mataimakinsa ne a kotu tun bayan da suka bayyana sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, The Nation ta ruwaito.

Kotun daukaka ta soke batun korar gwamna Umahi da mataimakinsa
Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi da Hukuncin Korar Gwamna Umahi da Mataimakinsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Dalilin da yasa ba za a kori gwamna mai ci ba, inji kotun daukaka kara

Kara karanta wannan

Malami Ya Bayyana Dalilai 4 da Yasa FG Ke Cigaba da Garkame Nnamdi Kanu

A hukuncinta na ranar Juma'a 28 ga watan Oktoba, kotun daukaka karar ta ce, babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi hukunci ga duk gwamna ko mataimakin da ya sauya sheka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, kotun ta ce ba tuni sashe na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba gwamna mai ci kariya da kuma garkuwa, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

A hukuncin, mai shari'a Haruna Tsanami ya bayyana cewa, dama daya da 'yan jam'iyyar da suka fusata suke da ita itace duba yiwuwar tsige gwamnan kamar yadda yazo a kundin tsarin mulkin kasa.

Hukuncin na kotun daukaka na Abuja dai ya yi daidai da wani hukuncin da kotu ta yanke a jihar Enugu.

MURIC Ta Bukaci a Dauke Cibiyoyin JAMB, WAEC Daga Cocunan RCCG

A wani labarin, kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta bukaci hukumomin jarrabawar WAEC da JAMB da su dauke cibiyoyinsu a cocin RCCG dake kan babbar hanyar Legas-Ibadan.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Bankado Kudi N20bn Mallakin Wani Shahrarren Dan Kasuwa a Legas

Kamar yadda yazo a rahoton Vanguard, daraktan MURIC, farfesa Ishaq Akintola ya bayyana bukatar dauke cibiyoyin ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba.

A sanarwar da ya fitar, Akintola ya zargi cocin RCCG da hana dalibai musulmai shiga Redemption City domin gudanar da hidimar jarrabawar WAEC da JAMB a harabarta.

Ya bayyana cewa, an hana dalibai musulmai shiga harabar domin kai takardun shaidan biya na banki, duba sakamakon jarrabawa da dai sauran lamuran da suka shafi jarrabawa a cibiyoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.