Tinubu Zai Ba Mata Dama Idan Ya Ci Zaben Shugaban Kasa, SWAGA

Tinubu Zai Ba Mata Dama Idan Ya Ci Zaben Shugaban Kasa, SWAGA

  • Shugaban ƙungiyar magoyan bayan Tinubu (SWAGA) yace ɗan takarar APC zai dama da mata a gwamnatinsa
  • A wurin kaddamar da shugabannin tsagin mata a Ogun, Sanata Adeyeye yace mata zasu sami mukamai masu gwabi idan Tinubu ya samu nasara
  • Shugabar matam SWAGA ta ƙasa, Ayo Omidiran, tace ya rataya a wuyan mata su tabbatar da nasarar Tinubu

Ogun - Shugaban ƙungiyar Southwest Agenda for Asiwaju (SWAGA), Sanata Dayo Adeyeye, yace mata zasu sami muƙamai idan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya lashe zaɓe mai zuwa.

Mista Adeyeye ya yi wannan furucin ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun yayin bikin kaddamar da sashin mata na SWAGA reshen jihar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Shilla Kasar Amurka, An Gano Babban Abinda Ya Fitar da Shi Najeriya

Asiwaju Bola Tinubu.
Tinubu Zai Ba Mata Dama Idan Ya Ci Zaben Shugaban Kasa, SWAGA Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Tsohon Ministan a Najeriya yace Tinubu, "Na girmama matan Najeriya," kuma ya yi alƙawarin ƙara yawan kason mata a sahun gaba na gwamnatinsa.

Ya kuma ayyana tsohon gwamnan jihar Legas ɗin da mutum mai hangen nesa da kuma aiwatar da aiki a aikace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa, Adeyeye yace:

"Asiwaju yace matan Najeriya zasu samu damarmaki masu tsoka a gwamnatinsa Insha Allah, rayuwarsu zata inganta fiye da kowane lokaci a tarihin ƙasar nan. Mata zasu shiga sahun gaba a gwamnatinsa."
"Ya ɗauki alƙawari kuma mun yarda da shi, ya kasance mutum mai tsantsar girmama mata, nan ba da jimawa ba zamu kai inda ake fata."

Oyetunji Ojo, wanda ya kirkiri tafiyar SWAGA yace sabbin shugabannin tsagin mata da aka kaddamar nauyi ne a kansu su haɗa kan matan SWAGA a matakin kananan hukumomi, gundumomi da mazaɓu.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin Da Yasa Duk Rintsi Ni da Mabiya Na Zamu Zabi Bola Tinubu, Babban Malami Ya Magantu

Ku shiga lungu da sako ku tallata Tinubu - Ojo

Ojo, mamban majalisar dokokin tarayya ya buƙaci matan su shiga lungu da sako na kasar nan domin tallata takarar Bola Tinubu.

Da yake ayyana Tinubu a matsayin wanda ya fi dacewa ya gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Ojo yace ɗan takarar APCn ya shirya sauya yanayin jagorancin Najeriya.

Shugabar sashin matan SWAGA ta ƙasa, Ayo Omidiran, tace mata na ɗauke babban nauyin tabbatar da Tinubu ya ɗare kujerar shugaban kasa.

A wani labarin An Faɗi Dalilin Da Yasa Cikin Sauki Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasan 2023

Jigon APC, Chief Sam Nkire, yace bisa la'akari da rashin zaman lafiya a PDP, Tinubu ba zai sha wahala ba a 2023.

Mista Nkire yace tarihi ya nuna cewa idan gwamnoni 5 suka yi bore a PDP ba ta kai labari, hakan ke shirin maimaita kansa.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tinubu Kan Kalaman Zama a Dubai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262