Yan Sanda Sun Kama Wani Mutumi da Katin Zabe Sama da 100 a Jihar Sakkwato
- Dakarun 'yan sanda sun yi nasarar ciki da wani mutumi ɗan yankin ƙaramar hukumar Sabon Birnin, jihar Sokoto ɗauke da katin zaɓe 101
- Kwamishinan yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ya yi kira ga mutane su zo su diba katunansu da suka bace
- A cewarsa bayan wata ɗaya zasu miƙa ragowar katunan ga hukumar zaɓe INEC idan masu su basu karɓa ba
Sokoto - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Sakkwato ta kama wani mutumi mai suna Nasiru Idris ɗan yankin ƙaramar Sabon Birni ɗauke da Katunan Zaɓe (PVC) guda 101.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kwamishinan 'yan sandan jihar, Hussain Gumel, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai ranar Alhamis.
Kwamishinan ya ce dakaru sun yi ram da wanda ake zargin ne a garin Sabon Birni ranar 10 ga watan Oktoba, 2022 biyo bayan samun kwararan bayanan sirri.
Hussain Gumel ya ƙara da cewa mutumin ya gaza ba da bayanin yadda ya tattara waɗannan katunan zaɓe da garuruwan da ya haɗasu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
kwamishinan yan sandan Sakkwato ya ce:
"Mun gano cewa masu Katin zaben ba mazauna ƙaramar hukumar Sabon Birni bane kaɗai ba, da yuwuwar masu katunan na zaune a wasu sassan jihar Sakkwato domin an gaza bibiyar asalin mamallaka katin PVCn."
Wane mataki hukumar yan sandan ta ɗauka?
Daga nan, CP Gumel ya yi kira ga ɗaukacin al'umma musamman waɗanda katin zaɓensu ya ɓata ko suka aje a wurin da bai kamata ba da su gaggauta zuwa Hedkwatar yan sanda su diba.
Yace hukumar yan sanda zata miƙa ragowar katunan da ba'a zo an karɓa ba ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) bayan wata ɗaya, Jaridar PM News ta ruwaito.
Bayan haka Legit.ng Hausa ta gano cewa hukumar 'yan sandan ta ƙara wa wasu jami'ai 6 matsayi.
A wani labarin kuma kun ji cewa ‘Yan Sanda Sun Damke Matasa 4 Dake Kwacen Ababen Hawa Tare da Siyar da Sassansu
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun yi caraf da wasu mutum 4 da ake zargi da kwarewa wurin kwacen ababen hawan jama’a a yankin Iganmu.
A bayanin da suka yi, suna kwace ababen hawan tare da tarwatsa su sannan su siyar dasu matsayin safaya ga dillalan kasuwar Ladipo.
Asali: Legit.ng