2023: Kashi 40 Na Mutanen Da Suka Yi Sabuwar Rijistar Zabe Dalibai Ne, INEC

2023: Kashi 40 Na Mutanen Da Suka Yi Sabuwar Rijistar Zabe Dalibai Ne, INEC

  • Jimilar mutum miliyan 3.8 wanda ya yi daidai da kashi 40.8 na wadanda suka yi sabuwar rijistar zabe dalibai ne
  • Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta kuma ce jimilar matasa miliyan 7.2 suka yi sabuwar rijista gabannin zaben 2023
  • Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba yayin ganawa da jam’iyyun siyasa

Abuja - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana cewa kaso 40 cikin dari na sabbin masu zabe da aka yiwa rijista duk dalibai ne.

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, ya kuma ce matasa ne kaso 76.5 na sabbin masu rijistar zaben, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jihohi 6 Mafiya Yawan Masu PVC Bayan INEC Ta Cire Sunan Mutum Miliyan 2.7

Mahmood Yakubu
2023: Kashi 40 Na Mutanen Da Suka Yi Sabuwar Rijistar Zabe Dalibai Ne, INEC
Asali: Original

Yakubu ya yi jawabi ne a taron zango na uku na 2022 wanda aka yi da jam’iyyun siyasa a dakin taro na INEC da ke Abuja.

A cewarsa, an samu karin sabbin masu zabe 9,518,188 kan 84,004,084 da ake da su kuma yanzu jimilar masu rijistan zabe a Najeriya ya kama 93,522,272.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“A karshen shirin, yan Najeriya 12,298,944 sun yi nasarar kammala rijinsta a matsayin sabbin masu zabe. Sau da dama mun ba yan Najeriya tabbacin
“Bayan mun kakkabe bayananmu ta hanyar amfani da tsarin ABIS, jimilar mutum 2,780,756 (22.6%) muka samu a matsayin wadanda basu cancanci rijista ba, a cikinsu akwai wadanda suka yi rijista fiye da sau daya, masu karancin shekaru da kuma masu rijistan bogi da suka ki cike tsarinmu.
“Hakazalika adadin masu ingantancen rijista shine 9,518,188.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya

“A bangaren shekaru, sabbin masu zabe miliyan 7.2 ko 76.5% matasa ne tsakanin shekaru 18-34 yayin da mata suka dan fi yawa (miliyan 4.8 ko 50.82%) maza su (miliyan 4.6 million ko 49.18%). A bangaren abun yi, miliyan 3.8 (40.8%) dalibai ne.”

Shugaban INEC din ya kuma bayyana cewa an gano jami’an da ke da hannu wajen yin rijista marasa inganci kuma za su fuskanci hukunci, rahoton TheCable.

Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na APC a Wata Jiha, Ta Yi Fatali da Wadanda Suka Ci Zabe

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Port Harcourt ta soke zaben fidda gwanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas, rahoton The Sun.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kotun ta zartar da hukuncin ne a jiya Litinin yayin sauraron wata kara da wasu fusatattun mambobin APCn suka shigar a gabanta.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Idan za a tuna, fusatattun mambobin sun yi zargin cewa an ware su a yayin zaben fidda gwanin jam’iyyar inda suka yi zanga-zanga sakatariyarta da ke Port Harcourt.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng