"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023
- Shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulkin kasa sun aikewa yan Najeriya sako
- Hakan na zuwa ne a yayin da kwamitin kamfen din zaben shugaban kasa na Kanada ta bukaci yan Najeriya su yi zabe da hikima a 2023
- Ba wai yin zabe kawai ba, kwamitin ta bukaci yan Najeriya su guji bada goyon bayansu da kada kuri'unsu ga mayaudaran yan siyasa a zaben mai zuwa
Watanni gabanin babban zaben shekarar 2023, kwamitin kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Kanada ta yi kira ga masu zabe su yi takatsantsan da yan siyasa da ke son karban mulki ta hanyar yaudarar mutane.
Hakan na cikin sanarwar da direktan watsa labarai na kwamitin, Abiola Oshodi, ya fitar ne a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, Legit.ng ta rahoto.
"Ku yi hankali da mayaudaran yan siyasa", APC ta gargadi yan Najeriya
A cewar The Punch, kwamitin kamfen din an kaddamar da ita ne don ganin nasarar jam'iyyar da dan takararta, Asiwaju Bola Tinubu, a babban zaben da ke tafe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban kwamitin, Jide Oladejo, wanda ya bada gargadin bayan kaddamar da kwamitin yakin neman zaben a Kanada, ya ce yan Najeriya a kasar ta Arewacin Amurka tuni suna goyon bayan dan takarar na APC.
Ya tabbatar da cewa:
"Bisa ga alamu, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na da abin da ake bukata don samar da sabuwar Najeriya tare da hadin kai da cigaba a Mayun 2023. Shekarun da jam'iyyar PDP ta yi tana mulki ne suka janyo matsalolin da ke adabar Najeriya.
"Masu zabe su yi hattara da yan siyasa wadanda suke kosa su yaudari yan Najeriya domin su mayar da Najeriya baya."
Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe
Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.
Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.
Asali: Legit.ng