Gwamna Wike Ya Rantsar Da Tsohon Kakakin APC da Wasu 17 a Matsayin Kwamishinoni
- Gwamna Wike ya rantsar da sabbin kwamishinoni 18 da ya naɗa a majalisar zartaswan gwamnatinsa
- Daga cikin mutanen dai har da tsohon kakakin jam'iyyar APC, Chris Finebone, wanda ya koma PDP a baya-bayan nan
- Gwamnan ya umarci kwamishinonin da waɗanda ke kan aiki tun kafin yau su fara harhaɗa bayanan miƙa mulki
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 18 da majalisar dokoki ta amince da su zuwa cikin majalisar zartaswan gwamnatinsa.
Daya daga cikin sabbin Kwamishinonin da suka karɓi rantsuwar kama aikin shi ne tsohon kakakin jam'iyyar APC, Chris Finebone, wanda ya sauya sheka zuwa PDP a baya-bayan nan.
Channels tv ta tattaro cewa daga cikin waɗanda gwamna ya naɗa har da tsofaffin Kwamishinonin da ya sallama daga bakin aiki a watan Mayun wannan shekarar.
Da yake jawabi ga Sabbin mambobin kwamitin zartaswan, Wike ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kammala wa'adinta da karfi da miƙa mulki ga wanda zai gaje shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kuma lura cewa wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwa ba su ɗaukar nauyin da aka ɗora musu da muhimmanci, maimakon haka sun gwammance su yi abinda ransu ke so su watsar da nauyin dake kansu.
Ku fara shirin mika mulki - Wike
Gwamna Wike ya kara nuna bukatar ganin gwamnatin ta mika mulki ga sabuwar zababbar gwamnati cikin ruwan sanyi kuma ta hanya mai kyau.
Bisa haka ya umarci sabbin kwamishinonin da waɗanda suka jima a gwamnati da tun wuri su fara harhaɗa bayanan da ya kamata domin rahoton ya kasance a shirye a lokacin da ya dace.
Jerin Kwamishinonin da suka karɓi rantsuwar kama aiki
Kwamishinonin da aka rantsar sun haɗa da Princewill Chike, Jacobson Nbina, Ndubuisi Okere, Inime Aguma, Charles Amadi, Tonye Briggs, Ben Daminabo, Chris Finebone, da Austin Chioma.
Sauran sune Uchechukwu Nwafor, Fred Kpakol, Emenike Oke, Prince Ohia, Kaniye Ebeku, Ezekiel Agri, Ukiel Oyaghiri, Damiete Miller da kuma Emeka Onowu.
Gwamnan yace Sakataren gwamnatin jihar, Tammy Danagogo, zai ba kowane kwamishina ma'aikatar da zai yi aiki.
A wani labarin kuma Hadimin Tambuwal, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Dandazon Mambobi Sun Koma APC
Makonni uku bayan fara kamfen 2023, jam'iyyar APC ta kara samun gagarumin goyon baya a jihar Sakkwato.
Hadimin gwamna Aminu Tambuwal da mataimakin shugaban PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da magoya bayansu.
Asali: Legit.ng