2023: Dalilin Da Yasa Na Fice PDP Zuwa APC Tare da Wasu Gwamnoni, Fani-Kayode
- Daraktan midiya na tawagar kamfen Tinubu, Femi Fani Kayode, yace ya zaɓi komawa APC ne saboda abinda yake tsoro ya kauce a jam'iyyar
- Tsohon ministan yace sheɗanun da suka dabaibaiye APC sun yi ƙaura zuwa PDP, shiyasa shi da wasu gwamnoni suka fita
- Yace zuwan gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya canza APC zuwa gidan kowa daga ko ina ka fito
Tsohon ministan Sufurin jiragen sama, Chief Femi Fani-Kayode (FFK) ya sake tsokaci kan dalilin da ya sa ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP).
Da yake jawabi a cikin shirin Politics Today na gidan Talabijin ɗin Channels TV, Fani-Kayode yace ya tattara komatsansa ya bar PDP ne saboda ta zama abin tsoron da yake tsammanin APC ke tattare da haka.
Tsohon ministan ya ƙara da cewa shaɗanin dake cikin jam'iyyar APC ya canza sheka ya koma ya tare a jam'iyyar PDP, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
A kalamansa yace:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Jam'iyyar APC da muka sani a baya ba ita ce a yanzu ba, sheɗanun APC a baya sun haɗe da PDP. A yau a APC ana mutunta kabilanci ba kamar a baya ba, bana tsoron faɗar gaskiya ina fatan kun fahimta?"
"Hangena daban a wancan lokaci har zuwa lokacin da lamarin ya canza, aka samu sabon shugabanci karkashin Mala Buni, gwamnan Yobe, sabbin mutane suka shigo, akwai gwamnonin da na sani suka ba ni tabbacin suna mutunta kowa."
"Mutane da yawa dake PDP a wancan lokacin da suka haɗa da Matawalle na Zamfara, Ayade na Kuros Riba, Umahi na Ebonyi da wasu gwamnoni sun sauya sheƙa har da ni kaina."
Meyasa FFK da Gwamnonin suka koma APC?
Fani-Kayode wanda shi ne daraktan midiya na tawagar kamfen Tinubu ya kara da cewa sun koma APC a wancan lokacin ne saboda abinda suke fargaba ya kau a jam'iyyar.
"Dalilin shi ne APC ta canza, abubuwan da muke fargaba sun kau. Mun ga lamarin ya zama PDP ce ke zama abin tsoron da a baya muke ganin APC haka take, an samu sauyi."
"Sun buɗe kofa tare da ba kowa damar ya zo a dama da shi kowane abu kai imani da shi kuma daga kowace kabila kake, kuma sun aiwatar a aikace."
A wani labarin kuma Tinubu Ya Bayyana Yan Takara Biyu Da Zasu Ba Shi Wahala a 2023, Ya Watsar da Kwankwaso
Ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, yace duk cikin yan takara, mutum uku ne fafatawa zata yi zafi a 2023.
Yayin ganawa da shugabannin ƙungiyar Tijjaniyya a Kano, Tinubu ya kira Atiku na PDP da mai yunkurin raba kawunan yan Najeriya.
Asali: Legit.ng