Siyasar Najeriya: An Bukaci Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, Ya Yi Murabus

Siyasar Najeriya: An Bukaci Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, Ya Yi Murabus

  • Babbar jam'iyyar hamayya a jihar Edo, watau APC ta yi kira ga gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya yi murabus nan take
  • Wannan kira na zuwa ne bayan gwamna Obaseki yace gwamnatinsa zata samu koma baya sakamakon maida hankali kan harkokin kamfe
  • Shugaban APC na jihar Edo, David Imuse, yace gwamnan ya gaza kuma mutane na fargabar halin da zasu shiga

Edo - Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Edo, Kanal David Imuse Mai ritaya, ya yi kira ga gwamna Godwin Obaseki ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Imuse ya yi wannan kiran ne yayin da yake martani ga kalaman da gwamna Obaseki ya yi ranar Jumu'a cewa gwamnatinsa zata samu koma baya sakamakon za'a maida hankali kan harkokin kamfen 2023.

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.
Siyasar Najeriya: An Bukaci Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, Ya Yi Murabus Hoto: Godwin Obaseki.
Asali: Facebook

Shugaban APCn yace idan Obaseki ya yi murabus zai ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) damar shirya sabon zaben gwamna a jihar, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Daba Ɗauke Da Bindigu Sun Kai Wa Ɗan Takarar Gwamnan PDP Hari

A wata sanarwa da mataimakin kakakin APC a Edo, Ofure Osehobo, ya fitar ranar Lahadi, shugaban jam'iyyar Wanda ya jima yana sukar gwamnatin, yace kiran ya zama tilas saboda fargabar da mutane ke yi cewa gwamnatin ta tsaya cak.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Imuse ya ƙara da cewa abun dariya ne irin waɗan nan kalmomin su fito daga harshen gwamna cewa gwamnati zata koma baya sakamakon zai maida hankali wajen tallata ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar.

Bugu da kari, ya yi ikirarin cewa tun kafin kalaman gwamna, Mutanen Edo sun jima da ɓaro jirgin Obaseki cewa dabaru da tunaninsa sun kare tun lokacin da aka rantsar da shi a zango na biyu.

Meyasa APC ta nemi Obaseki ya yi murabus?

Shugaban APC yace:

"Gwamna Obaseki ba ya zama a Benin City yayin da yake wayance wa da kokarin jawo masu zuba hannun jari ko sa hannun a yarjejeniya ko yin kamfe da ba shi ne ɗan takara ba."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

"Hakan ya ƙara tabbatar mana Demokariɗiyya ta raba gari da jihar Edo a yanzu ta koma mulkin kama karya karkashin jagorancin gwamna Obaseki, majalisa da ɓangaren shari'a, don haka muna kira ga gwamna ya yi murabus nan take."

A wani labarin kuma Kiristocin APC a Arewa Sun Yi kira Ga Kauracewa Kamfen Din 2023 Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi

Mambobin kungiyar kiristocin APC a Arewa sun yi kira da a gaggauta sauya Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu.

Kiristocin arewan sun bayyana kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a matsayin shirme kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262