PDP a Jihar Arewa Ta Yi Wa Atiku Abubakar Alkawarin Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Plateau ta dauki alkawarin kawowa Atiku Abubakar kuri'u miliyan biyu gabannin 2023
- Babbar jam'iyyar adawar kasar ta kuma sha alwashin lashe dukkanin kujerun siyasa a jihar
- Shugabannin jam'iyyar sun bayyana hakan ne a yayin kaddamar da kungiyar kamfen din Atiku-Mutfwang a Jos
Plateau - Jam’iyyar PDP a Plateau ta yi alkawarin kawowa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, kuri’u miliyan biyu a 2023 da kuma lashe duk wasu mukaman siyasa a jihar.
Jiga-jigan jam’iyyar a jihar sun bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Atiku-Mutfwang a Jos, babban birnin jihar, rahoton AIT.
Dandazon magoya bayan jam'iyyar sun halarci bikin kaddamar da kwamitin kamfen din na Atiku-Mutfwang gabbanin zaben 2023.
Dan takarar gwamnan PDP, Caleb Mutfwang, wanda ya kaddamar da kwamitin kamfen din ya ce zai jagoranci kawowa Atiku da duk yan takarar PDP a Plateau kuri’un jama’ar jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jawabinsa, shugaban PDP a jihar, Chris Hassan ya ce bikin kaddamar da kwamitin shine masomin kwato gwamnatin Plateau da Najeriya yayin da yake ba da tabbacin cewa Atiku zai samu fiye da kuri’u miliyan biyu a jihar.
A nasu jawain, tsohon jakadan Najeriya a Switzerland, Yahaya Kwande da sauran shugabannin jam’iyyar sun nuna karfin gwiwar cewa jam’iyyar za ta yi nasara a babban zaben mai zuwa.
Idan Atiku Ya Lashe Zaben 2023 Yan Kudu Sun Shiga Uku, Sagay
A wani labarin, shugaban kwamitin PACAC, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fallasa kansa a matsayin wanda ke kyamar yan kudu.
Sagay wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa mutanen kudu zasu dandana kudarsu idan har Atiku ya kashe babban zaben 2023 mai zuwa, rahoton Daily Independent.
Atiku, a wajen wani taron da kwamitin hadin gwiwa na arewa ya shirya, ya bukaci mutanen arewa da kada su zabi dan takarar shugaban kasa Bayarabe ko Ibo a zaben 2023.
Asali: Legit.ng