Mun Barwa Allah Ya Mana Zabin Magajin Buhari a 2023, Sarki Ya Fada Wa Atiku

Mun Barwa Allah Ya Mana Zabin Magajin Buhari a 2023, Sarki Ya Fada Wa Atiku

  • Babban Basaraken jihar Edo, Oba Na Benin, Oba Ewuare na II, ya faɗa wa Atiku cewa Allah suke roko ya zaɓa wa Najeriya shugaba
  • Basaraken yace suna saka Atiku Abubakar a addu'o'insu, ya roke shi ya cika alkawurran da ya ɗauka idan Allah ya ba shi mulki
  • Tsohon mataimakin shugaban kasan ya je Fadar Sarkin ne domin kwasar gaisuwa yayin da PDP ta yi kamfe a Edo

Benin City, Edo - Babban Sarkin Jihar Edo, Oba Na Benin, Oba Ewuare II, ya gaya wa dan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, cewa Allah ne zai zaɓi shugaban Najeriya na gaba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban Basaraken mai daraja ya yi wannan kalamai ne yayin da ya karɓi bakuncin Atiku da 'yan tawagarsa a fadarsa ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jam'iyyar APC Ta Fitar da Sunayen Tawagar Kamfen 2023 Na Karshe, An Samu Sauyi

Atiku Abubakar a fadar Sarkin Benin.
Mun Barwa Allah Ya Mana Zabin Magajin Buhari a 2023, Sarki Ya Fada Wa Atiku Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sarkin ya kuma yi wa Atiku fatan alheri a yunkurinsa na jagorantar Najeriya, kana ya bukaci ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa mutane lokacin kamfe idan Allah ya ba shi mulki.

Oba Ewuare na II yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ranka ya daɗe muna bibiyar kalamanka da alƙawurran da kake ɗauka, muna fatan Allah ya ƙara maka lafiya da hikimar da zaka cika maganganunka idan ka karbi mulkin ƙasar nan."
"Mun sanya ka a Addu'o'inmu, babu shakka zamu ci gaba da rokon Allah SWT ya zaɓa mana jagoran da zai shugabanci ƙasar nan. Babu dalilin da zai sa mu yi tababa kan ɗaya daga cikinku."

Ba zai yuwu mu zo Edo bamu kawo gaisuwa wurin iyaye ba - Atiku

Tun da farko, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ayyana Sarkin a matsayin ɗaya daga iyayen kasa dake taka muhimmiyar rawa wajen miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin demokaraɗiyga cikin ruwan sanyi.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

A ruwayar PM News, Atiku yace:

"Kana jagorantar babbar Masarauta mai ɗumbin tarihi, ba yadda zamu shigo jihar Edo ba tare da mun kawo gaisuwa ba. Saboda haka ina godiya a madadin tawagata bisa bamu lokacin da ka yi."

A wani labarin kuma Wike, Ortom, Makinde da Wasu Gwamnoni Sun Kaurace Wa Kamfen Atiku a Edo, Rikici Ya Kara Kamari a PDP

Gangamin taron yakin neman zaɓen shugaban kasa na PDP da ya gudana a jihar Edo ya kara fito da rikicin jam'iyyar.

Wasu gwamnoni dake kan madafun iko 5 sun kaurace wa taron, wasu kuma sun halarta ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262