Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC

Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar kwamitin gangamin tallata Bola Ahmad Tinubu
  • A yau ne ake bikin baje kolin manufofin da Tinubu ke cimmawa idan ya samu nasarar gaje Buhari a zaben 2023
  • Ana ci gaba da shirye-shiryen babban zaben 2023, lamarin da 'yan Najeriya da dama suka kagu da gani

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya na jagorantar taron kaddamar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar a gidan gwamnati dake Abuja.

Jaridar Punch ta ce ta samo cewa, an tsaurara tsaro a zagayen dakin taron, baki na shan fama wajen shiga cikinsa, ciki har da gwamnoni da manyan baki.

Buhari ya kaddamar da kwamitin gangamin kamfen Tinubu
Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An ga dandazon jama'a a bakin Banquet Hall na gidan gwamnati, ga kuma tulin jami'an tsaron farin kaya (DSS) dake kai komo a kewayen wurin, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Sha Alwashin Yi wa Tinubu Gagarumin Kamfen

A nasa jawabin, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, da irin shirin da jam'iyyar ta yi, tabbas za ta lallasa kowace jam'iyyar adawa a zabe mai zuwa badi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Baya ga kaddamar da kwamitin kamfen na Tinubu, Buhari zai kuma kaddamar da manufofin da wanda yake so ya gaje shi duk dai a taron.

Taron na kaddamar manufofin Tinubu ya samu halartar manyan jiga-jigan jam'iyyar APC daga bangarori daban-daban na Najeriya.

Jam’iyyar PDP Za Ta Gudanar da Taron Gangamin Kamfen Na Takarar Shugaban Kasa a Jihar Edo Ranar Asabar

A wani labarin kuma na daban, kinji cewa, tawagar kamfen din tallata dan takarar shugaban kasan PDP za ta karkata zuwa jihar Edo a ranar Asabar 22 ga watan Oktoba domin gudanar da gangamin lasawa 'yan Najeriya alkawuran Atiku.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bayan shafe kwanaki a Faransa, dan takarar PDP Atiku ya dawo Najeriya

Rahoton da muka samo daga jaridar Punch ya bayyana cewa, ana sa ran duk wasu jiga-jigan PDP za su hallara a filin taro da misalin karfe 10 na safiyar ranar.

Hakazalika, rahoton ya ce, dukkan gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar PDP za su hallara a wannan taro mai girma. Wannan batu dai na fitowa ne daga bakin babban daraktan gangamin kamfen din Atiku, gwamna Aminu Tambuwal, kamar yadda jaridar tace ta samo a jiya Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.