Idan Na Gaji Buhari, Zan Janye Jami’an Tsaro Ga Duk Masu Fada a Ji Kasar Nan, Inji Bola Tinubu
- Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga manufofinsa idan ya gaji Buhari
- Tinubu ya ce zai janye 'yan sandan dake ba manyan mutane kariya a fadin kasar don habaka aikin doka
- Ya kuma bayyana sabon tsarin da zai bi wajen tabbatar da tsaron manyan mutane, ta hanyar amfani jami'a NSCDC
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya yi alkawarin yiwa hukumar 'yan sanda garambawul idan aka zabe shi a 2023.
Ya bayyana cewa, zai daukewa 'yan sanda aikin zama dogarai ko 'yan gadi ga manyan mutane a Najeriya, inda ya kara da cewa, jami'an NSCDC ne za su ci gaba da wannan aikin.
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin takardar manufofinsa da jaridar Punch tace ta samo a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, manyan abubuwan da Tinubu ya sa a gaba sun hada magance batun tsaro, tattalin arziki, noma, makamashi, harkar mai, sufuri da kuma ilimi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shirin Tinubu bayan lashe zabe
A cikin daftarin da Tinubu ya tsara mai taken “Renewed Hope 2023 – Action Plan for a Better Nigeria,” yana kunshe da tsari da ka'idojin da zai tafiyar da gwamnati idan aka zabe shi.
Hakazalika, Tinubu ya ce zai habaka aikin 'yan sanda da sauran hukumomin tsaron cikin gida idan aka zabe shi, kuma zai dauki karin ma'aikatan tsaro a fadin kasar, Pulse ta tattaro.
A bangare guda, Tinubu ya ce zai samar da kayayyakin aiki na zamani kuma masu tafiya a turbar fasaha ga hukumomin tsaro.
'Yan takarar shugaban kasa a Najeriya na ci gaba da tallata muradai da shirye-shiryen da suke yiwa Najeriya idan aka zabe su a zaben 2023.
Tinubu, Obi Ko Atiku? Gwamna Wike Ya Fadi Irin Dan Takarar da Ya Kamata Kowa Ya Zaba a 2023
A wani labarin, gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi magana game da irin dan takarar da zai marawa baya a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamnan dake kai ruwa rana da Atiku ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar shugaban da zai kare muradan 'yan kasa baki daya ne ba wai wata kabila ba.
Ya ce, don haka wanda zai marawa baya dole ya kasance 'yan Najeriya a zuciyarsa, kuma zai yi aiki tukuru.
Asali: Legit.ng