Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci A Bangaren Kiwon Lafiya

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci A Bangaren Kiwon Lafiya

  • Shugaban kasa Buhari ya nada Dr Pokop Bupwatda a matsayin CMD na asibitin koyarwa na jami’ar Jos
  • Nadin Bupwatda a matsayin babban daraktan JUTH ya fara aiki daga ranar 30 ga watan Agustan 2022, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar
  • Mataimakin sashin labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta tarayya, Mista Ahmadu Chindaya, ya ce nadin na wa’adin shekaru hudu ne

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Pokop Bupwatda a matsayin babban daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin koyarwa na jami’ar Jos.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Ahmadu Chindaya, mataimakin sashin labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta tarayya ya saki a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Muhammadu Buhari
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci A Bangaren Kiwon Lafiya Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Chindaya ya bayyana cewa nadin Bupwatda na kunshe a cikin wata wasika dauke da sa hannun ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, Daily Trust ta rahoto.

An tattaro cewa wasikar ya fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Agustan 2022, kuma zai shafe tsawon shekaru hudu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake gabatar da wasikar ga Bupwatda, ministan ya bukace shi da ya jajirce don kawo ci gaba ga cibiyar don inganta tattalin arziki da kuma sauke nauyin da shugaban kasar ya daura masa.

Ehanire ya ce:

“Ma’aikatar lafiya ma’aikata ce mai muhimmanci ga fannin tattalin arziki, ka jajirce don inganta cibiyar lafiyar da ke karkashin kulawarka, ka dauki alhakin inganta tattalin arzikin da kuma yanayin asibitin koyarwar.”

Jawabin ya nakalto sabon CMD yana godiya ga shugaba Buhari kan ganin cancantarsa da ya yi sannan kuma ya bashi tabbacin cewa ba zai baiwa kasar kunya ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Taya Minista Pantami Murnar CIka Shekaru 50 A Duniya

Ya dauki alkawarin aiki da duk masu ruwa da tsaki domin inganta asibitin, rahoton The Nation.

Ana Tsaka Da Kukan Tsadar Abinci, Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Kara Tashi Da Kaso 20.77

A wani labarin, mun ji cewa ma'aunin farashin kayayyaki na CPI wanda ke gwada sauyin farashi a kayayyaki ya tashi daga 20.52% na watan Agusta zuwa 20.77% a watan Satumban bana.

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta fitar da hakan a bahasin kididdigar farashin kayayyaki karkashin CPI na watan Satumba, jaridar The Cable ta rahoto.

Adadin shine mafi yawa da aka taba samu tun a watan Satumban 2005.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng