Ana Tsaka Da Kukan Tsadar Abinci, Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Kara Tashi Da Kaso 20.77

Ana Tsaka Da Kukan Tsadar Abinci, Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Kara Tashi Da Kaso 20.77

  • Farashin kayayyaki a Najeriya ya kara tashin gauron zabi zuwa kaso 20.77 a watan Satumban 2022
  • Rahoton NBS ya nuna cewa an samu hauhawan farashin kayayyaki daga 20.52 da yake a watan da ya gabata
  • Hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana hakan ne a rahoton da ta fitar a yau Litinin, 17 ga watan Oktoba

Abuja - Ma'aunin farashin kayayyaki na CPI wanda ke gwada sauyin farashi a kayayyaki ya tashi daga 20.52% na watan Agusta zuwa 20.77% a watan Satumban bana.

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta fitar da hakan a bahasin kididdigar farashin kayayyaki karkashin CPI na watan Satumba, jaridar The Cable ta rahoto.

Kasuwa
Ana Tsaka Da Kukan Tsadar Abinci, Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Kara Tashi Da Kaso 20.77

Adadin shine mafi yawa da aka taba samu tun a watan Satumban 2005.

Kara karanta wannan

Tashin hakali: 'Yan kwangilar maganin yaki da Korona sun tsoho ma'aikata a Abuja, suna zanga-zanga

Hukumar NBS tace hakan na nufin an samu karin kaso 4.14 idan aka kwatanta da 16.63 da aka samu a watan Satumban 2021, wanda ke nuna an samu karuwa a Satumban 2022.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har ila yau tayi bayanin cewa hauhawan farashin ya samo asali ne daga tashin farashin kayan masarufi, tsaiko wajen samar da kayan abinci, kari a kudin shigo da kaya saboda lalacewar kudi dama kari a kudin kaya gaba daya.

Rahoton ya kuma ce farashin kayan abinci ya tashi zuwa kaso 23.34% a watan da ake magana a kai, hakan na nufin an samu karuwa idan aka kwatanta da 23.12 da aka samu a watan da ya gabata.

Hukumar ta kuma ce hauhawan farashin abinci ya samo asali ne daga karin da aka samu a farashin biredi, kayan hatsi, kayan abinci, dankali, doya, mai da sauransu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

Legit.ng ta zanta da wasu magidanta don jin yadda suke fama a wannan yanayi na tsadar rayuwa inda suka ce abun kawai sai rufin asirin Ubangiji.

Wani Magidanci mai suna mallam Abubakar yace yanzu rayuwa ta koma sai a hankali domin baya jin ta da dadi.

Ya ce:

“Ai wannan hali da muke ciki yanzu sai dai ace Innalillahi wa’inna illaihi raji’un. Talaka ya ga ta kansa. Kullun idan ka je kasuwa sai ka samu sauyi a farashin abubuwa.
“Ranar Asabar da ta wuce na je kasuwar gwadabe da ke nan Minna, N1,200 na auna kwanon shinkafa. Kuma fa shinkafa yar gida ba wai ta gwamnati ba. Dama kayan shayi yanzu ya fo karfin talaka, nawa ka siya madara, siga balle a kai ga biredi wanda idan baka da N700 ba za ka samu na ci a koshi ba. Allah dai ya kawo mana mafita.”

A nasa bangaren, Mallam Ibrahim cewa yayi:

Kara karanta wannan

Yanzu Fa Najeriya Bashi Muke Karba Mu Biya Bashi, Sanusi Lamido Sunusi

“Gaskiya tsadar kayan abinci ba karamar matsalar bace ga kananan ma'aikata irinmu. Dan abin da ka samu a madadin ka gyara tarbiyyar yara ka tura su makaranta mai kyau, duk mun karar a abinci, magani, da man abin hawa. Abinci babu sauki, kayan sakawa, kai hatta magani ma ba a barmu ba, abin dubu ya koma dubu biyar. Don Allah a kawo hanyar gyara tattalin arzikin kasar nan.”

Zaben 2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Zasu Yi Sauki, Sanusi Ga Yan Najeriya

A wani labari na daban, tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci yan Najeriya da kada su zabi duk dan takarar shugaban kasar da yayi ikirarin cewa abubuwa zasu yi sauki da zarar an zabe shi a 2023.

Sanusi wanda ya kasance shugaban darikar Tijanniya na kasa ya bayyana hakan a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wajen rufe taron tattalin arziki da zuba hannun jari na Kaduna, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wai Shan Man Fetur Muke yi: Sanusi Lamido Yace Ta Yaya Ake Shan Litan Mai Milyan 66 a Rana

Asali: Legit.ng

Online view pixel