Gwamna Wike Ya Kara Dagula Lissafin PDP Game da Dan Takarar Da Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Gwamna Wike Ya Kara Dagula Lissafin PDP Game da Dan Takarar Da Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

  • Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya shawarci yan Najeriya su zabi ɗan takarar shugaban ƙasa wanda ke da kwarewar shugabanci
  • Wike, wanda ya yi jawabi a wurin wani taro a Legas, yace ya kamata yan Najeriya su guji mutanen dake magana kan kabilanci
  • Duba da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP, babu tabbacin ko Wike zai goyi bayan takarar Atiku Abubakar a 2023

Lagos - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana irin nagartar ake bukata a jikin shugaban Najeriya na gaba yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.

Gwamnan yace ƙasar nan na bukatar shugaban ƙasa wanda yan Najeriya baki ɗaya ne suke a cikin zuciyarsa, sune tunaninsa a ko da yaushe.

Gwamna Wike a wurin taron matan Legas.
Gwamna Wike Ya Kara Dagula Lissafin PDP Game da Dan Takarar Da Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023 Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya faɗi haka ne ranar Talata 18 ga watan Oktoba, 2022 a wurin buɗe taron mata karo na 22 a jihar Legas, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu, Obi ko Atiku? Gwamna Wike ya fadi irin dan takarar da zai marawa baya

Wane ɗan takara ya kamata mutane su zaɓa a 2023?

Gwamna Wike ya roki 'yan Najeriya su taru su mara baya ga mutumin dake da kwarewar iya shugabanci, wanda zai iya haɓaka tattalin arziki kuma me kwarin guiwar fuskantar matsalar tsaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace:

"Muna neman shugaban ƙasa mai kwarewar iya shugabanci, wanda zai wadata kowa da abinci kuma ya yaki matsalar tsaro."
"Wannan ne irin mutumin da muke fata, ba mutanen dake magana kan kabilanci ba."

Jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida tun bayan bayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a watan Mayu.

Gwamna Wike, wnada shi ne Cibiyar baki ɗaya dambarwar, babu sahihin bayanin ko zai mara baya ga Atiku a zaben shugaban ƙasa dake tafe.

A wani labarin kuma Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Koma Bayan Obi a 2023

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Wani ɗan takara da ya nemi tikitin shugaban kasa a APC a 2019 ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi na jam'iyyar LP.

Charles Udeogaranya, yace takara Musulmi da Musulmi da APC ke kokarin ƙaƙabawa yan Najeriya wata makarkashiya ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262