Ana Wata Ga Wata a PDP, Shugabannin Jam'iyya a Edo Sun Yi Fatali da Tawagar Kamfen 2023
- Har yanzun zaman lafiya bai samu matsuguni ba a jam'iyyar PDP duk da kokarin da wasu kusoshi ke yi na kawo karshen rikicin
- A jihar Edo, shugabannin jam'iyyar sun fitar da sanarwan cewa sam ba su yarda da tawagar kamfe ta jihar da suka gani ana yaɗa wa ba
- A sanarwan, sun bukaci ɗaukacin magoya bayan PDP a Edo kar su ɗauki jerin sunayen da muhimmanci
Edo - Rikicin da ya addabi babbar jam'iyyar hamayya PDP ya kara tsananta ranar Talata yayin da shugabannin jam'iyya reshen jihar Edo suka haɗa kai suka yi fatali da sunayen mambobin kwamitin kamfe na jihar.
Jam'iyyar PDP a Edo tace ta yi watsi da jerin sunayen ne sabida ziyarar ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kewaye take da wasu kulle-kulle a ɓoye, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Sun yi watsi da jerin sunayen ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaba na jiha, Harrison Omagbon, da sakatare, Hillary Otsu, da shugabannin PDP na kananan hukumomi 18.
Haka zalika, sanarwan na ɗauke da sa hannun mambobin kwamitin ayyuka (NWC) na PDP ta jihar Edo aƙalla mutum 11.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwan tace:
"An jawo hankalinmu kan wani rahoto da jaridar Vanguard ta buga ranar 17 ga watan Oktoba, 2022 a shafi na 14 da 16. Mu mambobin NWC da shugabannin PDP na kananan hukumomi muna sanarwa magoya baya cewa:
"Bamu yarda da jerin sunayen mambobin kwamitin Kamfe da Vanguard ta buga ba. Babu wani ɓangaren jam'iyya da aka nemi shawarinsa wajen haɗa tawagar kafin a saki jerin."
"Ziyarar ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP kewaye take da kulle-kullen sirri a cikin gwamnatin Edo kaɗai. Muna kira ga mambobi su yi watsi da lamarin su maida hankali wajen taimaka wa yan takarar PDP a 2023."
Atiku da Bola Tinubu sun haɗu a Filin jirgin saman Abuja
A wani labarin kuma Bidiyon Abinda Ya Faru Yayin da Tinubu da Atiku Suka Haɗu a Filin Jirgin Sama
Manyan yan takarar shugaban ƙasa biyu dake sahun gaba, Bola Tinubu da Atiku Abubakar sun haɗu a filin jirgin sama a Abuja.
Bayanai sun nuna cewa jiga-jigan siyasar biyu sun gaisa da juna yayin da yan tawagarsu ke kiran sunan iyayen gidansu.
Asali: Legit.ng