Allah Sai Ya Tambaye Mu Idan Bamu Zabi Dan Takarar APC Tinubu Ba, Inji Kungiyar CAN Ta Legas
- Kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Legas ta ce, za ta fuskanci fushin ubangiji matukar bata goyi bayan Bola Ahmad Tinubu ba
- Rabaran Stephen Adegbite, shugaban CAN a Legas ya bayyana tasirin Tinubu, tare bayyana irin jajircewarsa a kasar
- Adegbite ya ce Tinubu ya ba kungiyar CAN gudunmawa sosai a lokacin da yake gwamnan jihar Legas a shekarun baya
Jihar Legas - Shugabancin kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Legas ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Wannan batu na goyon baya na fitowa ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba daga bakin shugaban CAN na Legas, Rabaran Stephen Adegbite, inji rahoton jaridar Independent.
A nasa fahimtar, shugaban na CAN ya ce, tabbas Allah zai hukunta duk wani kirista a karkashin CAN ta Legas da ya ki goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa.
Ya bayyana cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Allah zai kama mu idan bamu goyi bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba.
"Na shaidawa abokanmu na shiyyar Arewa cewa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne dan takararmu kuma za mu goyi bayansa."
CAN reshen jihar Legas za ta goyi bayan Tinubu
Malamin na coci ya bayyana cewa, babu wanda zai taka ma CAN ta jihar Legas birki wajen goyon bayan burin Tinubu na gaje Buhari saboda irin gudunmawar da ya ba kungiyar a yankin Kudu maso Yammaci.
Ya tuna yadda tsohon gwamnan na Legas ya kirkiri shirin daukar nauyin kiristoci zuwa birni mai tsarki na Jerusalam duk shekara, kuma har yanzu hakan na aiki, rahoton BluePrint.
A kalamansa:
"Babu wanda ya isa yace mana kada mu goyi bayan Bola Ahmed Tinubu saboda ya yi abubuwan da suka wuce misali wajen tallafawa kiristoci a Kudu maso Yamma."
Kungiyoyin kiristoci a Arewacin Najeriya na nuna adawa da dan takarar APC na shugaban kasa tun bayan da ya zabi Musulmi a matsayin abokin takara.
Jerin Jihohin da a Za a Kai Ruwa Rana a Zaben Gwamnan 2023 Mai Zuwa
A wani labarin, akalla a jihohi 17 ne cikin 28 za a iya samun zaben gwamna mai tsauri a 2023 kasancewar gwamnoni masu ci a jihohin ka iya aiki tukuru don ganin sun daura 'yan takarar da suke so su gaje su.
Gwamnoni 17 ne a Najeriya suke kan wa'adi na biyu na mulki, kuma daidai da ka'idar INEC, za su sauka a zaben 2023 don daura sabbin masu jan ragama a jihohinsu.
Abu ne a bayyane, wasu gwamnoni ka iya kokari wajen kawo magajin da suka zaba suke so domin ci gaba daga inda suka tsaya.
Asali: Legit.ng