Shugaban Kasa A 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ta Bayyana Jihohin Arewa 3 Da Peter Obi Ka Iya Lashe Zabe
- Ba lallai ne ace Peter Obi yana da karfin lashe zabe ba, amma dai dan takarar na jam’iyyar LP zai zamo barazana ga wasu abokan hamayyarsa
- Daga cikin wadanda ke sane da cewar Obi na iya sauya tsarin siyasar Najeriya harda jiga-jigan jam’iyyar APC
- Mataimakiyar kakakin jam'iyyar APC, Hannatu Musawa, ta bayyana cewa Obi na iya kawo jihohin Benue, Plateau da Taraba a 2023
Duba ga yadda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ke kara samun farin jini, jam'iyyar APC ta yi wasu hasashe game da abubuwan da ka iya faruwa a babban zaben mai zuwa.
Mataimakiyar kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, ta bayyana cewa Obi na iya lashe wasu jihohin arewa da duk wani dan takara ke bukatar kuri'unsu don lashe zabe.
Ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da jaridar The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba.
Peter Obi na iya lashe zabe a Benue, Plateau da Taraba
Da take bayyana cewa da arewa ne dan takara zai lashe zabe ko ya fadi a zaben shugaban kasar, Musawa ta bayyana cewa jihohi irin su Benue, Plateau da Taraba na iya zabar tsohon gwamnan na jihar Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musawa ta ce:
"A arewa ne za a lashe ko faduwa a wannan zaben. Haka abun yake. Wannan shine gaskiyar batu, ko muna so ko bama so.
"Abun da ake bukata bisa ga tanadin kundin tsarin mulki da dokar zabe ba wai kawai ka samu mutane miliyan da zasu yi maka gangami bane. Dole ne ka samu wasu adadi na kuri'u daga jihohi.
"...Bana ganinsa a matsayin wanda zai lashe kowace jiha a arewa, banda jihohi Benue, Plateau da watakila Taraba, da ake bukata don lashe zaben kasa... "
Zaben 2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Zasu Yi Sauki, Sanusi Ga Yan Najeriya
A wani labarin, tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci yan Najeriya da kada su zabi duk dan takarar shugaban kasar da yayi ikirarin cewa abubuwa zasu yi sauki da zarar an zabe shi a 2023.
Sanusi wanda ya kasance shugaban darikar Tijanniya na kasa ya bayyana hakan a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wajen rufe taron tattalin arziki da zuba hannun jari na Kaduna, The Cable ta rahoto.
Asali: Legit.ng