Yakasai: Ba Zan Iya Muzanta Ganduje Ba Duk Da Ya Kwace Mukamin Da Ya Bani

Yakasai: Ba Zan Iya Muzanta Ganduje Ba Duk Da Ya Kwace Mukamin Da Ya Bani

  • Salihu Tanko Yakasai, dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar PRP a zaben 2023 ya ce ba zai iya cin dunduniyar Gwamna Ganduje na Kano ba
  • Yakasai, tsohon hadimin gwamna Ganduje ya ce gwamnan tamkar uba ya ke a wurinsa baya ga aikin da ya masa na shekaru shida
  • Dawisu, kamar yadda aka fi saninsa a Twitter ya ce Ganduje ya sallame shi ne don faranta wa wasu manya a gwamnatin tarayya rai amma ba don ya soki gwamnatin Kano ba

Kano - Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a bangaren watsa labarai, ya ce ba zai taba cin dunduniyarsa ba.

Daily Trust ta rahoto cewa sau biyu Ganduje ya sallami Yakaisai kan kalaman suka da ya yi game da yadda ke tafiyar da batun tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Tsohon da Yayi Shekaru 47 da Barin Kasarsa Ya Dawo Gida Babu Arzikin da Yaje Nema

Yakasai da Ganduje
Yakasai: Ba Zan Ci Dunduniyar Ganduje Ba Duk Da Ya Sallame Ni. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da ya sa ba zan zagi Ganduje a bayansa ba

A yayin da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa bai taba fadin maganganu marasa kyau game da gwamnan a yanzu ba ya masa aiki, Yakasai ya ce akwai alaka irin ta da da mahaifi tsakaninsa da Ganduje baya ga aiki na shekara shida da ya masa.

Ya kara da cewa gwamnan bai sallame shi saboda ya soki gwamnatin jiha ba amma sai don maganganun da ya yi game da gwamnatin tarayya, yana zargin an kore shi don farantawa manya a kasar rai.

Yakasai, wanda ya yanke ya ke takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PRP, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron tattaunawa da kungiyar yan jarida na kasa reshen jihar Kano ta shirya gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Ya ce:

"Ba zan iya cin dunduniyar mai gida na ba saboda banbancin siyasa. Ban yarda da irin wannan siyasar ba. Mun shafe shekara shida muna aiki, ya sallame ni ne saboda magana da na yi kan gwamnatin tarayya ba gwamnatinsa ba."

Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisu a Twitter ya karyata zargin cewa Gwamna Ganduje ne ya dauki nauyin takararsa a PRP don APC ta samu saukin cin zabe.

2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

A wani rahoton, mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.

Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba Goodluck ne alherin da Najeriya ta taba gani a tarihi, inji gwamnan Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164