Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Bayyana Dalilin Rashin Ganin Sunanta Tawagar Kamfe Ta Mata

Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Bayyana Dalilin Rashin Ganin Sunanta Tawagar Kamfe Ta Mata

  • Shugabar matan APC ta kasa ta yi karin bayani kan dalilin rashin shigarta tawagar kamfen mata na zaɓen 2023
  • Dakta Betta Edu tace ba zai yuwu a ganta cikin sahun tawagar matan ba a matsayinta na mace lamba ɗaya a APC
  • A ranar Litinin da ta gabata ne jam'iyyar APC ta kaddamar da jirgin tallata Bola Tinubu na mata karƙashin Aisha Buhari

Abuja - Shugabar matan jam'iyyar APC ta ƙasa, Betta Edu, ta bayyana cewa zai saɓa wa hankali idan aka ga sunanta a jerin tawagar kamfe ta mata, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Jam'iyyar APC mai mulki ta fitar tare da ƙaddamar da tawagar yakin neman zaɓe ta mata karkashin jagorancin uwar gidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari.

Shugabar matan APC ta ƙasa, Betta Edu.
Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Bayyana Dalilin Rashin Ganin Sunanta Tawagar Kamfe Ta Mata Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mai ɗakin Bola Tinubu kuma Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya, Oluremi Tinubu, da Nana Shettima, matar abokin takarar Tinubu, su ne zasu yi aiki a matsayin shugabanni.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Kalaman da Tinubu Ya Nemi Tawagar Matan APC Su Faɗa Wa 'Yan Najeriya Masu Neman Canji a 2023

Sai dai bayan fitar da sunayen, ƙungiyar magoya bayan jam'iyyar APC (APCSG) ta yi ƙorafin cewa babu sunan shugabar matan jam'iyya ta ƙasa, Betta Edu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa babu sunan Edu a tawagar?

Da take karin haske kan batun ranar Talata, shugabar matan tace hakan ta faru ne saboda matsayinta a jam'iyyar, aikinta shi ne ta sa ido kan harkokin tawagar ƴaƙin neman zaɓen.

"Abu ne mai sauƙi kuma a fili, ni ce Dr. Betta Edu kuma shugabar matan APC ta ƙasa, mace lamba ɗaya a jam'iyya mai mulki saboda haka abun zai saɓa wa tunani a ga sunana karƙashin wasu da ya kamata su kasance ƙasa na a APC."
"Don haka aikina shi ne na Kula, duk wani abu da ya shafi mata, taruka, haɗa kai da jawo hankalin mutane duk ni zan sa ido a kai. Wannan Tawagar da zata tallafi kamfe ce wanda za'a kaddamar nan gaba kaɗan."

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

"Ku tuna, wannan tawagar kamfen mata ce ba wai asalin kwamitin ba saboda haka baki ɗayansu suna karkashin jam'iyyar APC ne. Mu ne motar muna da fasinjojin da zasu tuƙa."

- Betta Edu.

A wani labarin kuma Sanata Ya Gargadi PDP Kar Ta Yi Kuskuren Watsi da Wike, da Wasu Gwamnoni 4

Sanata Chimaroke Nnamani, ya gargaɗi shugabannin PDP kada su tafka kuskuren watsi da gwamnoni biyar da suka fusata.

Tsohon gwamnan jihar Enugu yace gwamna Wike da takwarorinsa huɗu da suka kauracewa taron PDP sun fi karfin a jingine su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel