Takara a 2023: Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Ya Fadi Matsayarsa Ta Karshe Kan Hukuncin Kotu

Takara a 2023: Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Ya Fadi Matsayarsa Ta Karshe Kan Hukuncin Kotu

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, yace bai da niyan daukaka kara kan hukuncin kotu kan takararsa a zaben 2023
  • Hadimin shugaban majalisar dattawan, Ola Awoniyi, yace tun farko ya fito ya bayyana matsayin ubangidan nasa na amsar hukuncin kotun hannu bibbiyu
  • Babbar kotun tarayya ta Damaturu dai ta hana Lawan shiga takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa karkashin APC a zabe mai zuwa

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bai da niyan daukaka kara kan hukuncin kotu da ya haramta masa takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa a zaben 2023.

Mai ba shugaban majalisar dattawan shawara na musamman kan harkokin labarai, Ola Awoniyi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a Abuja, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ba harka: Dan takarar shugaban kasan wata jam'iyya ya tsorata, zai janye daga takara

Ahmad Lawan
Takara a 2023: Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Ya Fadi Matsayarsa Ta Karshe Kan Hukuncin Kotu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Sanarwar ta ce:

“Mun ga wani rahoto da ke yawo a yanar gizo daga Sahara Reporters game da takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na APC a zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Rahoton ya yi ikirarin cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya lashe amansa kan hukuncin da ya yanke da farko na kin daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu a jihar Yobe ta yanke wanda ya soke takararsa a zaben.”

Jawabin ya kuma bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege inda ya jadadda cewa shugaban majalisar dattawan bai da niyan daukaka kara kan hukuncin kotun.

Ya kuma ce idan wani ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotun sannan ya yanke shawarar daukaka kara, toh lallai wannan bai da alaka da shugaban majalisar dattawan, rahoton Vanguard.

Ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudi a Yau, Tsaro ya Tsananta a Farfajiyar Majalisa

“Shugaban majalisar dattawan ya bayyana matsayinsa a idon duniya kuma tuni ya ci gaba da harkokinsa. Shi mutum ne mai magana daya. Don haka muna umurtan jama’a da su yi watsi da rahoton karya na Sahara Reporters.”

Dalilai Biyu Ne Suka Ja Ahmad Lawan Ya Rasa Tikitin Takarar Sanata a Yobe

A baya mun ji cewa rikicin ko wanene zai zama dan takarar sanatan da hukumar zabe ta INEC ta amince dashi a APC a mazabar Yobe ta Arewa ya kawo karshe, domin an zabi Bashir Machina a matsayin dan takara.

Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Fadima Murtala Aminu ta yanke hukunci a yau Laraba 28 ga watan Satumbam inda ta umarci INEC ta amince da Machina a matsayin dan takarar sanatan APC daga Yobe ta Arewa.

Tikitin takarar dai an jima ana kai ruwa rana akansa tsakanin Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa da Bashir Bachina tun bayan kammala zaben fidda gwanin APC.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel