Zaben 2023: APC Ta Shirya Tsaf, Ta Sanar d Ranar Kaddamar da Tawagar Kamfe Ta Mata
- Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa zata fara buɗe Kamfen shugaban ƙasa da ƙaddamar da tawagar yakin mata ranar Litinin
- Tawagar yaƙin neman zaɓe ta mata ta kunshi uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, a matsayin jagora
- Jagoran APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ne ke neman zama shugaban ƙasa a inuwar APC
Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta kammala duk wasu shirye-shirye na buɗe fagen yaƙin neman zaɓe ranar Litinin, inda zata fara da kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta mata.
Jam'iyyar APC, ta bakin kwamitin shirye-shirye na jirgin mata da zasu tallata Tinubu/Shettima, tace za'a kaddamar da mambobin tawagar ranar Litinin a Aso Rock.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, ita zata ja ragamar tawagar yaƙin neman zaɓen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa.
Matar dan takarar shugaban ƙasa kuma Sanata tsawon zango uku mai wakiltar Legas ta tsakiya, Oluremi Tinubu, da matar Sanata Kashim Shettima, Hajiya Nana Shettima, su ne zasu shugabanci tafiyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanar da tawagar kamfen mata ya haddasa martani masu daɗi daga kowace kusurwar ƙasar nan, inda da yawan 'yan Najeriya ke mamakin meyasa sauran jam'iyyu ba su ware wa mata fagensu a yaƙin zaɓe.
Wasu kuma na ganin tawagar yaƙin neman zaɓe ta mata da APC ta sanar mai kunshe da mambobi 1, 200 daga lungu da saƙo na kasar nan ya ƙara fito da yunkurin APC na ba kowane jinsi dama.
Legit.ng ta tattaro cewa jam'iyyar APC ce ɗaya tilo a cikin manyan jam'iyyun siyasa da take da mace mai neman zama gwamna a babban zaɓen 2023.
Wasu majiyoyi masu ƙarfi daga cikin APC sun ce za'a bai wa tawagar mata damar cin gashin kanta a fagen Kamfe, zasu shirya tarukansu kana su gudanar da harkokinsu a matakin gunduma, karamar hukuma da ƙasa.
"Bayanai sun ce mata na ci gaba da kokarin aiwatar da gangamin dubbannin mambobi daga ƙungiyoyin magoya baya daban-daban a shirinsu na jawo hankalin masu kaɗa kuri'a," inji majiya.
Idan gwamnoni suka tsame hannunsu ba zamu kai labari ba - Adamu
A wani labarin kuma Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023
Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace idan har gwamnoni suka zare hannunsu jam'iyyar ba zata kai labari ba a 2023.
Tsohon gwamnan jihar Nasarawa yace nasarar APC na hannun Allah kuma tana hannun gwamnoni.
Asali: Legit.ng