Zaben 2023: APC Ba Ta Da Halastacen Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Ku Zabi Atiku, PDP Ga Yan Najeriya
FCT, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba ta da halastacen dan takarar shugaban kasa, a cewar jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP), Daily Trust ta rahoto.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a hedkwatar jam'iyyar a ranar Asabar, Debo Ologunagba, sakataren watsa labarai na kasa na PDP, ya ce soke takarar gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya tabbatar da matsayar jam'iyyar na cewa dukkan yan takarar da shugabanni da Gwamna Mai Kala Buni na Yobe ya samar ba su hallata ba.
Makon da ya gabata, babban kotun tarayya da ke Abuja ta soke zaben Gwamna Isiaka Oyetola da mataimakinsa, Benedict Alabi, a matsayin yan takarar APC a zaben gwamna na jihar Osun.
2023: Babban Matsala A Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Gabatar Da Hujja, Ya Shigar Da Kara Don Soke Takarar Tinubu Da Atiku
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai shari'a Emeka Nwite, alkalin kotun, ya soke zaben Oyetola da mataimakinsa ne kan cewa Buni, wanda ya mika wa mutanen biyu tikiti, ya saɓa doka na rike muƙamai biyu a hukumance a lokaci guda akasin tanadin kudin tsarin mulki.
Ologunagba ya ce hukuncin babban kotun tarayyar na nufin duk wani aiki da Buni ya yi, har da sa ido kan zaben da ya samar da Abdullahi Adamu, shugaban APC da zaben fidda gwani da ya samar da nasarar Tinubu duk na su halasta ba, don haka an soke su.
Don haka ya yi kira ga ƴan Najeriya kada su yi asarar kuri'ar su, amma su zabi ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Ologunagba ya ce Tinubu ba shi da wani abu da zai yi wa yan Najeriya amma ya koma gida ya fuskanci "matsalolin rashin tsayar da magana daya game da karatunsa, sunansa, asalinsa, shekaru da zargin rashawa."
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng