Babbar Kotu Ta Haramta Wa Yan Takara 12 Shiga Babban Zaben 2023 a Jiha Daya
- Babbar Kotun tarayya dake zama a Patakwal ta haramta wa yan takara 12 na majalisar dokokin jihar Ribas shiga zaɓen 2023
- Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ce ta kai ƙarar masu neman takarar gaban Kotu bisa zargin sun karya sabon kundin dokokin zaɓe
- Hukuncin Kotun ya shafi yan takara 7 na jam'iyyar ADC da kuma guda 5 na jam'iyyar ADP
Rivers - Babbar Kotun tarayya dake zama a Patakwal ta soke tikitin 'yan takarar majalisar jihar Ribas 12 na jam'iyyun African Democratic Congress (ADC) da Action Democratic Party (ADP).
Jaridar Punch tace alƙalin Kotun, mai shari'a Turaki Mohammed, ya amince tare da abinda jam'iyyar PDP ta gabatar masa cewa jam'iyyun sun karya dokokin zaɓe 2022 yayin gudanar da zaben fidda gwaninsu.
Kotu ta soke tikitin yan takarar ADC guda Bakwai
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a baya jam'iyyar PDP ta shigar da ƙarar masu neman zama mambobin majalisar jihar Ribas su 12 karkashin inuwar ADC bisa zargin saɓa wa doka.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake yanke hukunci, Mai Shari'a Muhammed, yace hukumar zaɓe INEC ba ta da hurumin amincewa da 'yan takarar majalisar jiha 7 a inuwar ADC saboda hujjojin da aka baje masa sun nuna cewa jam'iyyar ta yi wa doka hawan kawara.
Lauyan ADC, Benibo, yace tawagar lauyoyi zasu yi nazari kan hukuncin Kotun, sannan su ɗauki matakin ko zasu ɗaukaka ƙara ko a'a.
"Ina tunanin Alkali ya gano cewa jam'iyya ba ta ayyana a fili kan kalar zaben fidda gwanin da zata yi ba, 'yar tiƙe, na Deleget ko maslaha. Yan takara 5 sun tsira yayin da Bakwai kuma suka rasa tikitinsu."
"Wataƙila zamu ɗaukaka ƙara saboda INEC ta na da bayanai, ta san irin zaɓen da aka aiwatar. Amma zamu zauna mu duba hukuncin, idan akwai ƙofar ɗaukaka ƙara zamu tafi gaba, wuƙa da nama na hannun jam'iyya."
A ɓangarensa, Lauyan PDP, Dike Udenna, yace wasu daga cikin zaɓukan fidda gwanin jam'iyyar INEC ba ta da masaniya kan yadda aka gudanar da su.
Mazaɓun da jam'iyyar ADC ta rasa yan takara sun haɗa da, Tai, Onelga, Etche da kuma Ahoada duk na majalisar dokokin jihar Ribas.
Kotu Ta Soke tikitin yan takara 5 na ADP
Haka zalika, babbar Kotun dake zama a Patakwal ta haramta wa mutum 5 dake neman zama mambobi a majalisa tarayya a inuwar ADP shiga zaɓe saboda jam'iyyarsu ta karya kundin dokokin zaɓe.
Yayin da aka kira batun, Mai Shari'a Muhammed yace PDP ta gamsar da Kotu cewa INEC bata sa ido a zaɓukan da suka ayyana mutanen a matsayin yan takarar ADP ba, bisa haka tikitin bai halatta ba.
Mazaɓun da lamarin ya shafa sun haɗa da Emohua, Eleme, Bonny, Omuma, da kuma Oyigbo. Shugaban ADP na Ribas, Christian Kendrick, yace nan da yan kwanaki zasu sanar da mataki na gaba.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Sanar da Ranar Kaddamar da Tawagar Kamfen Tinubu Ta Mata Karkashin Aisha Buhari
Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa zata fara buɗe Kamfen shugaban ƙasa da ƙaddamar da tawagar yakin mata ranar Litinin.
Tawagar yaƙin neman zaɓe ta mata ta kunshi uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, a matsayin jagora.
Asali: Legit.ng