Zaben 2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na Babban Jam'iyya Ya Bayyana Abu Guda Ɗaya Da Zai Gyara Najeriya
- Adewole Adebayo, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP a zaben 2023 ya ce gaskiya kadai za ta iya gyara Najeriya
- Adebayo ya furta hakan ne a jawabin da ya yi wurin taron da cibiyar jagoranci da ayyukan sojoji ta shirya a ranar Talata a Abuja
- Dan takarar shugaban kasar na SDP ya ce dukkan yan Najeriya suna da laifi kan jefa kasar halin da ta shiga kuma yan kasar za su iya gyara ta
Abuja - Gabanin babban zaben shekarar 2023, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, Prince Adewole Adebayo, ya ce gaskiya ne kadai za ta iya gyara Najeriya, Daily Trust ta rahoto.
Ya bayyana hakan ne wurin taron da cibiyar jagoranci da ayyukan sojoji ta NDA ta shirya da aka yi a Cibiyar Sojoji ta, NARC, ranar Talata a Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, idan ana son a gyara abu, dole a dakatar da cigaba da bata shi.
Adebayo ya ce:
"Ya kamata ka fahimci abin da ya lalace. Kasar mu ba kasa ce mai wuyar rayuwa a ciki ba. Matsalar shine wasu mutane suka lalata kasar da gangan. Yan Najeriya ne kadai za su iya gyara kasar kuma sune suka lalata kasar.
"Abin da ya kamata mu fara gyarawa shine kan mu. Za mu shiga zaben ne ba don mu koyi darrusa ba sai dai don lokaci ya yi. Mutane na cewa Buhari matsala ne. Suna son su ce Jonathan waliyyi ne. Ban yarda ba. Daya ya ke da Obasanjo.
"Abin da zan fada wa yan Najeriya daya yake da abin da zan fada wa makanike na. Ka san matsalar motar? Idan baka san matsalar Najeriya ba, ba za mu iya gyarawa ba."
Karfin hali: Bidiyon baturiyar da tazo har Najeriya ta siya turmi da tabarya ta koma turai ya jawo cece-kuce
Ya kuma ce wasu mutane na son gyara kasar, ba komai suke son gyarawa ba.
Gaskiya ce kawai za ta iya gyara Najeriya - Adebayo
Ya ce:
"Kamar duk matasa suna fushi da Najeriya. Kamar matasan ba su da laifi. Amma, ko muna so ko ba mu so, kowa na da laifi. A bangare na, ina son gyara kasa ta. Sifana ta ita ce gaskiya. Ba abin da zai amfane ni kawai na ke yi ba. Muna da matsalar tsaro. Gwamnat mai ci za ta iya tsayar da matsalar idan ta dakatar da kasuwancin da ke cikinsa."
Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP
A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na Accord Party, AP, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.
Asali: Legit.ng