Keyamo Ya Ce Bai San Inda Tinubu Ya Ke Ba A Halin Yanzu
- Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya ce bai san inda dan takarar jam'iyyarsu ya ke ba
- Karamin ministan kwadago da samar da ayyukan ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a Channels TV a daren ranar Laraba
- Keyamo, amma ya ce dan takarar shugaban kasar na jam'iyyarsu zai dawo cikin yan kwanan nan duk da cewa bai fada rana ba
Kakakin kwamitin kamfen na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Festus Keyamo, a daren ranar Laraba ya ce bai san inda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Bola Tinubu, ya ke ba a yanzu.
Hakan ne zuwa ne a lokacin da yi karyata hasashen da ake yi na cewa tsohon gwamnan na jihar Legas ya fita kasar waje don a duba lafiyarsa.
Keyamo, wanda ya yi wannan karin hasken lokacin da ake hira da shi a shirin 'Politics Today' na Channels TV ya ce masu makirci ne kawai suke matsuwa game da inda Tinubu ya ke, ya kara da cewa babu wanda ya damu lokacin da dan takarar shugaban PDP, Atiku Abubakar ya tafi Dubai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Keyamo: Ban san inda Tinubu ya ke ba a yanzu amma zai dawo cikin yan kwanakin nan
Ya ce:
"Dan takarar mu a halin yanzu baya kasar kuma ban da masaniya kan inda ya ke a halin yanzu. Na san zai dawo cikin yan kwanakin nan amma ban san takamamen ranar ba.
"Kuma ba duba lafiya ya tafi ba; ban da wannan bayanin. Ba gaskiya bane cewa ba mu fara kamfen ba saboda dan takarar mu ba shi da lafiya kuma baya nan."
Da aka masa tambaya ko bidiyon da Tinubu ya wallafa a baya-bayan nan ya yi da wata manufa ne, karamin ministan na kwadago da ayyukan yi ya amsa da cewa:
"Iya sani na kai tsaye aka nadi bidiyon aka wallafa a shafinsa na Twitter. Ba wai don a nuna yana da rai bane. Dan takarar mu ba kokarin gamsar da wani ya ke ba. Na kusa da shi sun san shi ma'abocin tuka keken ne, ya saba hakan."
Ya kuma kara da cewa ba wai masu makirci bane za su rika saka su yin abubuwa, ya kara da cewa suna da tsarinsu kuma a kan shi za su rika tafiya.
A Aljanna Ne Kawai Ba Za A Samu Matsalar Tsaro Ba, Yanzu Kuma Duniya Muke, Ministan Buhari, Keyamo
A wani rahoton, Festus Keyamo, ya ce ba za a iya amfani da 'hare-haren' da aka kaiwa wasu sassan kasar ba a matsayin 'mizani' na cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.
Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke
Keyamo ya yi wannan jawabin ne a hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Juma'a, The Cable ta rahoto.
Asali: Legit.ng