Babu Jam'iyya Mai Nagarta Kamar PDP a Najeriya, Atiku Ya Magantu a Gangamin Bauchi

Babu Jam'iyya Mai Nagarta Kamar PDP a Najeriya, Atiku Ya Magantu a Gangamin Bauchi

  • Mai neman zama shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, yace babu jam'iyya a Najeriya da ta zarce PDP ta ko wane fanni
  • Tsohon mataimakin shugaban kasan ya samu kyakkyawar tarba daga cincirindon magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar Bauchi
  • Shugaban PDP na ƙasa da na jihar Bauchi, Dino Melaye da wasu jiga-jigai sun halarci gangamin

Bauchi - Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, yace babu wata jam'iyya mai nagarta da ta zarce PDP a faɗin Najeriya.

Channels tv ta ruwaito cewa Atiku ya yi wannan magana ne yayin da yake jawabi ga cincirindon magoya bayan PDP a wani gangami da aka shirya masa a Bauchi.

Atiku a Bauchi.
Babu Jam'iyya Mai Nagarta Kamar PDP a Najeriya, Atiku Ya Magantu a Gangamin Bauchi Hoto: @Atiku
Asali: Twitter
"Babu jam'iyyar da ta kai PDP a ƙasar nan, mu ne muka fi daɗe wa a tarihi, muka fi ƙarfi kuma muka fi girma."

Kara karanta wannan

Allah Muke Roko Ya Bamu Mafi Alheri Tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso - Sarkin Hausawan Awka

"Saboda haka ina mai amfani da wannan damar wajen taya al'ummar Bauchi murna da gwamna Bala Muhammed bisa wannan nasara kuma na yi imani cewa idan muka fara kamfen shugaban kasa, zamu ga abinda ya zarce haka."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Atiku Abubakar.

Jiga-Jigan PDP da suka halarci gangamin

Bayan mai masaukin baki gwamna Muhammed na Bauchi, waɗanda suka halarci gangamin sun haɗa da shugbaan PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, shugaban PDP na jiha, Hamza Akuyam, Dino Melaye da sauran ƙusoshi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya karbi dubbannin masu sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP a jihar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Atiku, ɗan shekara 75 a duniya daga jihar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya, na neman zama shugaban ƙasa a 2023 tare da manyan yan takarar kamar Bola Tinubu na APC da Peter Obi.

Kara karanta wannan

2023: Matsala Ga Tinubu, Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Koma Bayan Atiku da PDP a Jihar Arewa

Ya kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓensa ranar 28 ga watan Satumba, 2022 amma kusan gwamnoni 5 da suka fusata basu halarci wurin ba.

A wani labarin kuma Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace idan har gwamnoni suka zare hannunsu jam'iyyar ba zata kai labari ba a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa yace nasarar APC na hannun Allah kuma tana hannun gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262