An Sake Duba Sunayen Kwamitin Kamfen din Tinubu, Adamu ya ki Halarta

An Sake Duba Sunayen Kwamitin Kamfen din Tinubu, Adamu ya ki Halarta

  • Tawagar yakin neman zaben Tinubu da Shettima, sun yi zama a Abuja inda suka tattauna kan sunayen dake kwamitin
  • Sai dai an gano cewa, Sanata Adamu da wasu daga jiga-jigan jam'iyyar APC basu halarci taron ba duk da ya dace a zauna da su
  • Simon Lalong ya jagoranci taron inda ya bayyana cewa suna duba sunayen ne domin kwantarwa da gwamnonin APC hankali da wasu mambobin

FCT, Abuja - Masu tsarin tawagar kamfen din kujerar shugabancin kasa na Tinubu da Shettima sun yi ganawar sirri a Abuja a ranar Talata da yammaci inda suka sake duba jerin sunayen mambobin kwamitin.

Taron da ya samu shugabancin gwamnan jihar Filato, Gwamna Simon Lalong, wanda shi ne darakta janar na kwamitin, an fara shi ba da wuri ba a ofishin PCC dake Abuja.

Kara karanta wannan

Iyorchia Ayu Ya Dawo da Zafinsa, Ya Bukaci Ayi Bincike Kan Shugabannin Jam’iyya

Tinubu da Adamu
An Sake Duba Sunayen Kwamitin Kamfen din Tinubu, Adamu ya ki Halarta. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Wata majiya ta sanar da The Punch cewa ajandar wadanda suka samu halartar taron ta tsaya kan bukatar su sake duba jerin sunayen domin gujewa caccakar da wasu fusatattun gwamnonin APC da mambobin NWC bayan sunayen farko sun bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daraktan yada labarai na PCC, Bayo Onanuga, ya tabbatar da hakan ga jaridar Punch kan cewa Lalong ne ya kira taron domin a sake duba jerin sunayen.

"Amma taron cikin gida ne. An yi shi ne domin sake duba jerin sunayen tawagar kamfen din ta yadda jama'a ba za su cigaba da korafi ba. Wannan shi ne makasudin taron."

- Yace.

Sai dai babu wasu mambobin NWC wadanda suka hada da shugaban jam'iyya ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu da ya halarci taron a ranar Talata.

A yayin da aka tambaya ko mambobin NWC ya dace su halarci taron, wata majiya tace in har ba yarjejeniya aka yi ba, suna da hurumin halartar taron.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: BoT na PDP ta kammala zama da gwamnan da ke ba Atiku ciwon kai

Yace:

"Su ma ai mambobin PCC ne. Ku tuna Adamu shi ne mataimakin shugaban kwamitin sannan wasu mataimakan shugaban jam'iyyar na kasa su ne kodinetocin da mataimakin shugabannin shiyya.
"Amma da yawa daga cikinsu basu halarci taron ba. Sai dai na gane cewa akwai taro muhimmi da za a yi na NWC a gobe Laraba domin zantawa kan sunayen."

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

A wani labari na daban, 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ba zai samu damar saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2023 ba.

Tinubu, wanda a yanzu haka yana kasar Birtaniya, ba zai samu halartar taron saka hannu kan yarjejeniyar da kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ya shirya ba,wanda shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ke shugabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng