Abinda Zan Yi Idan Na Dare Kujerar Shugaban Kasa a 2023, Kwankwaso

Abinda Zan Yi Idan Na Dare Kujerar Shugaban Kasa a 2023, Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya sha alwashin cewa idan ya ci zaɓe zai dawo da martabar Najeriya
  • Kwankwaso, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar NNPP yace a baya mutane sun yi hasashen ba zai kai labari
  • Ɗan takarar ya nuna damuwarsa kan yadda matasa ke zaman kashe wando, wasu suka fara shaye-shaye

Taraba - Ɗan takarar shugaban kasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya sha alwashin dawo da ɗaukakar Najeriya idan aka zaɓe shi a 2023.

Kwankwaso Ya faɗi haka ne jim kaɗan bayan gana wa da ƙusoshin jam'iyyar NNPP a Jalingo, babban birnin jihar Taraba ranar Lahadi, inda ya buɗe sabbin ofisoshin jam'iyyar.

Rabiu Musa Kwankwaso.
Abinda Zan Yi Idan Na Dare Kujerar Shugaban Kasa a 2023, Kwankwaso Hoto: KwankwasoRM
Asali: Twitter

A shafinsa na Tuwita, Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa ya jagoranci taro da shugabannin NNPP na jihar, inda suka tattauna batutuwan sake gina Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Faɗi Abinda Ya Faru Lokacin Marigayi Yar'Adua

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace yana da kwarewar canza akalar Najeriya da dawo da zaman lafiya da manyan ayyukan raya ƙasa. Wannan a acewarsa ya ingiza shi ya shiga tseren takara.

"Kun gani, dabarun mu shi ne mu bar mutane su rinka tunanin ba zamu taɓuka komai ba, tsarukan mu na karkashin kasa bamu sake su a iska ba. Yan Najeriya na ganin masoyan mu, waɗanda suka sadaukar da kansu."
"Mutanen da suka yi imani da aƙidarmu, sun san idan aka bamu dama, muna da kwarewar canza abubuwa da dama zuwa kan turba, saboda haka sun san idan muka hau mulki ƙasar nan zata gyaru."

- Rabiu Kwankwaso.

Mun ba mutane da yawa mamaki - Kwankwaso

Kwankwaso ya ƙara da cewa a watannin da suka gabata, da yawan mutane na ganin ba zasu kai labari ba a zaɓen shekara mai zuwa, a halin yanzun yace lamarin ya canza.

Kara karanta wannan

2023: Mun Gano Kuskuren Da Muka Tafka, Atiku Ya Magantu Kan Rikicin PDP da Su Gwamna Wike

"Watanni Bakwai baya da muka shiga jam'iyyar nan, da yawan mutane na ganin ba zamu je ko ina ba amma da ikon Allah kowa ya san mu a ƙasar nan yanzu."

Ɗan takarar NNPP yace duk da ya yi wa shugaba Buhari kamfe ba ya jin daɗin rashin ayyukan yi a tsakanin matasa, wanda a cewarsa ya jefa wasu cikin harkar shaye-shaye da fashi.

A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Shiga Matsala, 'Yar Takarar Gwamnan Jiha Da Ta Lashe Tikiti Ta Fice daga NNPP

Mace ɗaya tilo da jam'iyyar NNPP ta tsayar takarar gwamna a zaɓen 2023 ta sanar da janye wa daga tseren takara.

Jackie Adunni Kassim, mai neman zama gwamnan jihar Ogun a NNPP tare da magoya bayanta sun fice daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262