2023: PDP Ta Mutu Murus, Babu Sauranta a Jihata, Gwamnan Ebonyi

2023: PDP Ta Mutu Murus, Babu Sauranta a Jihata, Gwamnan Ebonyi

  • Gwamnan jihar Ebonyi dake kudu maso gabashin Najeriya yace babu sauran jam'iyyar PDP a jiharsa
  • A watan Nuwamban shekarar 2020, David Umahi ya sauya sheƙa zuwa APC bayan lashe zaɓen gwamna sau biyu karƙashin PDP
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa jinkirta kamfen APC ba zai cutar da nasararta ba, zasu zo da sabbin tsaruka nan ba da jima wa ba

Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, kudu maso gabashin Najeriya, yace babu sauran ɓurɓushin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a faɗin jiharsa.

The Cable ta tattaro cewa a watan Nuwamba, 2020, gwamna Umahi ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC, inda ya kafa hujja da yi wa yankin kudu maso gabas, "Rashin adalci."

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi.
2023: PDP Ta Mutu Murus, Babu Sauranta a Jihata, Gwamnan Ebonyi Hoto: thecable
Asali: Twitter

Kafin wannan lokaci, Umahi ya rike muƙamin mataimakin gwamna kuma ya lashe zaɓen gwamna sau biyu duk a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Faɗi Abinda Ya Faru Lokacin Marigayi Yar'Adua

Da yake jawabi a cikin shirin Sunrise Daily, shirin kafar talabijin ɗin Channels tv ranar Litinin, Gwamna Umahi ya yi ikirarin cewa PDP ta mutu murus a jihar Ebonyi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Umahi yace:

"Kowace jiha na ginuwa ne a kan tubalin kokarin da gwamna ya yi. Na yi matukar kokari kuma lamarin bai shafi jam'iyya ba, ya danganci jagorancin jihar."
"Babu sauran PDP a jihar Ebonyi, kuma idan idonku ya gane muku tarukan mu na baya-bayan nan, kun ga adadin yawan mutanen suka fito. Saboda haka PDP ba ta da harshen da zata iya magana."
"A halin yanzu ba su ne na biyu ba a jihar Ebonyi, don haka babu wata PDP ko tsarinta."

Meyasa aka jinkirta Kamfen APC?

Gwamnan yace jinkirin da aka samu game da fara yaƙin neman zaben shugaban ƙasa ba zai illata damar da APC ke da ita na lashe zaɓe mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

2023: Mun Gano Kuskuren Da Muka Tafka, Atiku Ya Magantu Kan Rikicin PDP da Su Gwamna Wike

"Muna da sauran watanni gabanin zuwan ranar zaɓe kuma muna da watanni da zamu yi kamfe. Wanda ya fara ba lallai bane ya fara gama wa."
"Jam'iyyar APC banki ce kuma zamu zo da sabon Salo da tsaruka, nan ba da jima wa ba zaku ga ya faru."

A wani labarin kuma Lado Ɗanmarke Ya sha alwashin dawo da zaman lafiya a Katsina cikin wata uku idan ya ci zaɓen 2023

Mai neman zama gwamnan Katsina a inuwar PDP, Yakubu Lado, ya bayyana muhimman abubuwa biyu da zai sa a gaba.

Sanata Lado yace da zaran ya ɗare madafun iko a 2023, zai tasa matsalar tsaro a gaba don kare rayukan al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262