Bola Tinubu Ne Ya Fi Cancantar Zama Shugaban Kasa, Inji Uba Sani
- Dan takarar gwamnan APC a jihar Kaduna ya bayyana dan takarar shugaban kasan APC a matsayin jigon dimokradiyya
- Sanata Uba Sani ya ce tabbas Tinubu ne ya fi cancanta ya gaje kujerar shugaban kasa Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya a 2023
- Jam'iyyar APC ta tsayar da Asiwaju Bola Ahmad a matsayin gwaninta da zai gwabza a zaben 2023, Sanata Kashim Shettima ne abokin gaminsa
Kaduna - Dan takarar gwamna a jihar Kaduna a jam'iyyar APC, Uba Sani ya ce dan takararsu na APC da ke neman gaje kujerar Buhari ne mafi cancantan zama shugaban kasa a zaben 2023.
Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoton cewa, jam'iyyar APC ta tsayar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasan a zabe mai zuwa nan da badi.
Uba sani, wanda sanata ne mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, ya ce Tinubu ya yi amfani da karfi da dukiyarsa wajen ciyar da dimkoradiyya gaba a kasar nan yayin da wasu 'yan takarar kuma tubabbun 'yan mulkin soja ne.
A cewar dan takarar gwamnan, wannan lokaci ne da ya kamata a ba Tinubu dama ya zama shugaban kasa saboda zai ciyar da kasar gaba ainun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Uba Sani ya bayyana hakan ne a wani bikin karramawa ta mazauna Kaduna 'yan asalin jihar legas da ya a ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba, Punch ta ruwaito.
A kalamansa:
"Ba zai yiwu mu kwatanta Tinubu da sauran 'yan takaran shugaban kasa ba, saboda babu su a lokacin da Asiwaju ke fafutukar tare da mutane kamar mu wajen tabbatar da dimokradiyyar da yanzu muke mora."
Tasirin Tinubu a jihar Legas
Shugaban kungiyar ta mazauna Kaduna 'yan asalin jihar Legas, Sheriff Olutusin ya gina ababen more rayuwa da ilmantar da jama'a tare da kawo sauye-sauye a jihar Legas, The Nation ta ruwaito.
Hakazalika, tsohon gwamnan na Legas ne ya habaka tattalin arzikin Legas daga N600m zuwa N50bn da ma dai sauran ayyukan ci gaba a jihar.
Taron ya samu halartar baki da mawakan da suka karbi lambobin yabo kamar su dan gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai, CSP Idiyat Olugbeja mai ritaya, Alhaji Pa Lander Akanbi Lawal da Sheikh Ibrahim Al-Imam Shittabey da da sauransu.
Malamin Coci Ya Yi Nadama, Ya Nemi Gafara Saboda Karbar Kudin Shan Ruwa a Hanya Daga Hannun Tinubu
A wani labarin, Rabaran Danjuma Byang, mamba daga manyan malaman addinin kirista daga Arewa da suka wakilci tawagar Pentecostal wajen ganawa da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana kadan daga abubuwan da suka tattauna a kai.
Jairdar The Guardian ta ruwaito cewa, malamin ya rubuta wata wasikar nuna nadama a kafar WhatsApp, inda ya fasa kwai kan tattaunawarsu da Tinubu.
An zargi malaman na coci daga Arewa da cike aljifansu da kudi bayan da suka gana da Tinubu.
Asali: Legit.ng