2023: Zamu Baiwa Tsaron Katsinawa da Manyan Ayyukan Raya Kasa Fifiko, Lado Danmarke
- Mai neman zama gwamnan Katsina a inuwar PDP, Yakubu Lado, ya bayyana muhimman abubuwa biyu da zai sa a gaba
- Sanata Lado yace da zaran ya ɗare madafun iko a 2023, zai tasa matsalar tsaro a gaba don kare rayukan al'umma
- Yace gwamnatin APC ta ƙarar da baki ɗaya dabarunta kuma ko da ta sake kafa gwamnati ba zata iya magance komai ba
Katsina - Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, yace gwamnatins zata maida hankali wajen tsare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Daily Trust ta ruhoto Yakubu Lado na cewa matuƙar Kashinawa suka damƙa masa amana a 2023, zai fifita tsaro da manyan ayyukan rasa ƙasa.
Lado, wanda ya yi wannan furucin yayin hira da manema labarai a Abuja a ƙarshen makon nan, yace matsalar tsaro ta dakushe shugabanci ta ko wane fanni.
Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari
Ɗan takarar ya jadda da cewa kalubalen nan wata rana zai zama tarihi matuƙar an ɗauki kwararan matakan da suka dace wajen fuskantarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanata Yakubu Lado ya ce:
"Jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta ƙarar da basira da dabarunta kan yadda zata magance matsalolilin nan, haka za'a ci gaba da wahala da matsalolin idan har APC ta sake kafa gwamnati a shekara mai zuwa."
"Idan har aka bani dama na zama gwamna, zan kawo karshen kalubalen tsaron da ya addabi jihar mu cikin abinda bai wuce watanni uku ba."
"Ba zan faɗi asalin shiri na game da dawo da zaman lafiya ba, zan bar shi a zuciyata har zuwa lokacin saboda batu ne na tsaro."
Wani jigon PDP a ƙaramar hukumar Ɗanja, jihar Katsina kuma masoyin Lado, Kabir Abdullahi, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa jam'iyyarsu ta shirya koma wa madafun iko don gyara ɓarnar APC.
Abdullahi, ya yaba da kyakkyawan nufin Yakubu Lado na magance ƙalubalen tsaron da ya hana mutane walwala a jihar, inda ya jaddada maganar ɗan takarar cewa zaɓen PDP jihadi ne a 2023.
"Insha Allahu duba da irin dandazon mutanen dake ficewa daga APC a Katsina, PDP zata kwace mulki a 2023. Yakubu Lado mutum ne mai nagarta ga kyauta kuma ya yi an gani," inji shi.
A wani labarin kuma Sanatan PDP Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Faɗi Abinda Ya Faru Lokacin Marigayi Yar'Adua
Sanatan Adamawa ta kudu, Binos Dauda Yaroe, yace akwai bukatar sauya manyan shugabannin PDP na ƙasa.
Yaroe mai wakiltar mazaɓar da Atiku ya fito, ya roki tsagin Wike su yi koyi da abinda ya faru a 2007 lokacin marigayi Yar'adua.
Asali: Legit.ng