An Ga Bidiyon Atiku Na Tikar Rawa, Manufofinsa Biyar Sun Bayyana

An Ga Bidiyon Atiku Na Tikar Rawa, Manufofinsa Biyar Sun Bayyana

  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce ba za a kodimo babu shi ba, an ganshi yana tika rawa a wani bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta
  • Dan takarar shugaban kasan na jam'iyyar PDP ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana kadan daga manufofinsa na gyara Najeriya
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi martani bayan ganin bidiyon, tare da alakanta da shi da na Bola Tinubu lokacin da yake motsa jiki

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya cancare da rawa tare da bayyana manufofinsa na gyara Najeriya guda biyar inda aka zabe shi ya gaji Buhari.

Atiku dai ya sha bayyanawa balo-balo cewa, shi ya cancanci jan ragamar Najeriya bayan zaben 2023 da ake ta shirin yi nan gaba a lokuta mabambanta.

Atiku na tika rawa a wani bidiyon da aka yada
An Ga Bidiyon Atiku Na Tikar Rawa, Manufofinsa Biyar Sun Bayyana | Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

A cikin bidiyon mai dauke da sautin wakar Davido da aka yada a kafar Twitter, an nuna manufofin Atiku guda biyar kamar haka:

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa ya fadi abu daya zai yi ya magance yajin ASUU

"Kare Najeriya, habaka tattalin arzikinmu, inganta fannin ilimi da kwarewa, saka fasalin gwamnatinmu don yin aiki yadda ya dace da kuma karfafa hadin kanmu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai biyo bayan wannan bidiyo, 'yan Najeriya da dama sun yi martani tare da bayyana ra'ayoyinsu kan manufofin Atiku.

Wasu Sunce Na Mutu, Sunce Na Janye, Amma Kwalelenku Ina Nan Lafiya: Tinubu

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi watsi da jita-jitan da ake cewa jinya ya tafi birnin Landan.

Tinubu ya saki sabon bidiyon da dan tsokaci a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba, 2022.

Bidiyon mai tsayin sakwanni bakwai kacal ya nuna Tnubu yana motsa jiki kan keken tafi da gidanka cikin dakinsa a Landan.

A jawabin da yayi, Tinubu yace:

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu ya ce zai ba 'yan Najeriya mamaki, zai sauya makomar Najeriya

"Wasu da dama sun ce na mutu; wasu sun ce na janye daga kamfen neman shugaban shugaban kasa."
"Amma kash! Gaskiyan magana shine ina da karfi ne, ina cikin koshin lafiya kuma shirye nike da bautawa yan Najeriya tun ranar farko."

PDP Ta Tabbatar da Tura wa Mambobin NWC Miliyoyin Kudi, Amma Ta Ce Ba Cin Hanci Bane

A wani labarin, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta amince da cewa ta tura wasu miliyoyi zuwa asusun bankunan mambobin kwamitinta na ayyuka (NWC), amma ta musanta ba da kudin a matsayin cin hanci.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, martanin na PDP na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.

Rahoton ya ce, sanarwar da PDP ta fitar martani ne ga kalaman wasu mambobi da ke cewa sun mayar da N20m da aka basu tare da alanta cin hanci aka basu don zama kan wata magana.

Kara karanta wannan

Kamfen zaben 2023: Tinubu ya fadi sassan da zai tafi yawon kamfen a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.