Bincike Na Musamman Kan Takardun Karatun Peter Obi Ya Bayyana Ainihin Sunansa
- Tattaunawa kan takardun makarantun yan takarar shugaban kasa ya zama batu da ke daukan hankalin mutane
- A cikin watanni da suka shude, wasu yan takarar sun bayyana cewa ba su san inda satifiket dinsu ya ke ba hakan ya janyo cece-kuce
- Amma, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya banbanta domin takardun karatunsa sun bayyana a dandalin sada zumunta
Twitter - A yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2023, ana ta karo da dirama a jam'iyyun siyasa daban-daban a Najeriya.
Cikin abubuwan da suka rika daukan hankulan mutane akwai sakamakon zabukan fidda gwani, zargin bawa daliget toshiyar baki, musayyar maganganu da wasu abubuwan.
Amma, daya daga cikin abin da mutane suka yawaita cece-kuce a kansa gabanin babban zaben 2023 shine batun takardun shaidan karatu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A baya-bayan nan, wasu yan takarar sun gaza gabatar da satifiket dinsu inda suka bada uzuri na cewa sun bata ko kuma wasu dalilan.
Wasu manyan sunaye da wannan lamarin ta shafa sun hada da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na YPP, Abdulmalik Ado Ibrahim, dan takarar shugaban kasa na ADP, Sani Yabagi da sauransu.
Takardar shaidar digiri (BSc) da NYSC na Peter Obi sun bayyana
Kazalika, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, shine dan takarar shugaban kasa na farko da ya fara bayyana satifiket din digiri dinsa da na yi wa kasa hidima wato NYSC.
Legit.ng ta gano digiri dinsa da tsohon jakada kuma jigon LP Oseloka Obaze ya wallafa.
Ga rubutun da ya wallafa tare da satifiket din.
"Ga shi don wadanda suke son su tabbatar da digiri din @PeterObi. Sauran yan takarar suma su yi hakan."
Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa
Bayanan da ke cikin takardar digiri din sun nuna tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi karatu a Jami'ar Najeriya, Nsukka a 1984 ya kammala da second-class lower a Falsafa, kuma sunansa "Gregory Peter Ouwubuasi Obi".
2023: Peter Obi Ya Bayyana Shirin Da Ya Yi Wa Yan Bindiga, Da Masu Neman Ɓallewa Daga Ƙasa Idan An Zaɓe Shi
A wani rahoton, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya sha alwashin ba zai yi sasanci da yan bindiga ba idan an zabe shi shugaban kasa a babban zaben 2023, The Cable ta rahoto.
Peter Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba yayin hira da aka yi da shi a Arise TV.
Yayin da ya ke magana a hirar na talabijin, ya ce idan aka zabe shi gwamnatinsa za ta tattauna da masu neman ballewa daga kasa da wasu masu ruwa da tsaki.
Kwararan Majiyoyi Sun Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa APC Ta Dakatar Da Fara Kamfen Har Sai Baba Ta Gani
Asali: Legit.ng