Da Nine Shugaban Kasa, ASUU Ba Za Su Fara Batun Yajin Aiki Ba, Inda Dan Takarar Shugaban Kasa a Accord
- Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana kadan daga irin abin da ya shirya don gyara fannin ilimi da ya gurbace a Najeriye
- Dan takarar na jam'iyyar Accord ya ce a karkashin kulawarsa, dole zai sauya kowane fanni a ma'aikatar ilimin Najeriya
- Ya kuma ce, idan ana maganar yajin ASUU, babu yadda za a yi ya bari kungiyar ta malaman jami'a su fara tafiya yajin aiki
Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Accord, Farfesa Christopher Imumolen ya bude wasu daga kudurorin da ke ransa kuma ya shirya yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari.
Farfesan kuma fitaccen dan kasuwa ya bayyana manufar tasa ce a bikin yaye daliban cibiyar JTPS, wata cibiyar karatun gaba sakandare da ke birnin Legas a kwanakin baya.
Da yake fashin baki ga tamboyin 'yan Najeriya, farfesa ya ce a matsayinsa na wanda ya san harkar gudanar da makaranta, ya ce lamarin koyo ga dalibai zai zama mai sauki a mulkinsa.
A fahimtarsa, a lokacin da makarantu ke garkame na tsawon watanni saboda malaman jami'a na yajin aiki, ya ce zai samar da hanyoyi masu kyau na inganta harkar ilimi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, ya ce shirinsa zai kawo mafita ga matsalolin tsaro da yankin Arewacin Najeriya ke fuskanta cikin gaggawa, kamar yadda Legit.ng ta samo.
A cewarsa:
"Kasancewar mun samu damar yaye dalibai daga cibiyar a daidai lokacin da akasarin daliban makarantunmu ke zaman dirsham a gida na tsawon watanni saboda yajin aikin ASUU shaida ce mai nuni da cewa ilimi zai habaka idan aka samar da ka'idojin da zasu kare martabarsa.
"To, abin da nake fadi a takaice shi ne, ya kamata a zamanantar da fannin iliminmu a fasahance. Yanzu zamani na fasaha. Dole mu fara kauracewa tsohon yayin zaman aji kawai tare da fara koyo daga ko'ina ta hanyar amfani da fasaha.
"Hakazalika, muna bukatar zuba kudi a bangaren. A yanzu haka, muna kashe 6.4% kacal ne abin da muke samu a matsayin kasa ga fannin ilimi. Wannan bai watadar ba. Abin kunya hakan ya yi kasa da sharadin da majalisar dinkin duniya ta ba kasashe game da fannin ilimi.
"Idan na zama shugaban kasa, zan tabbatar da samar da 20% na kasafin kudin shekara don ba fannin ilimi
"Bugu da kari, idan na zama shugaban kasa, zan yi kokari wajen kawo dokokin da za su ba fannin ilimi 'yancin cin gashin kansa domin bude kofa ga masu zuba hannun jari, domin habakawa da kawo gaza a fannin lafiya da zai saukaka kudaden da fannin ilimi ke ci a kasar."
Zan Jagoranci Najeriya Zuwa Ga Makoma Mai Kyau, Inji Dan Takarar APC Tinubu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga abubuwan da ya shirya idan ya gaji Buhati bayan zaben 2023.
Ya matukar 'yan Najeriya suka zabe shi tare da abokin takarar sanata Kashim Shettima, to tabbas goben Najeriya za ta yi kyau ainun, Punch ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba 28 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa, zai shiga lungu da sakon Najeriya domin tallata hajarsa ga kwadayin dalewa kujerar Buhari.
Asali: Legit.ng