2023: Zan Sadaukar Da Kaina Ga Jihar Katsina, Dan Takarar APC Dikko
- Mai neman zama gwamnan Katsina a inuwar APC, Dikko Radda, yace a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa don gyara jihar
- Tsohon shugaban hukumar SMEDAN yace yadda ya ɗauki siyasa ba haka take ba, daga lokacin da aka tsayar da shi takara komai ya canza
- Radda ya nuna damuwa kan yadda 'yan siyasa ke yaudarar mutane, a cewarsa da yawa ba don Allah suke yi ba
Katsina - Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a zaben 2023 ƙarƙashin inuwar APC, Dakta Dikko Umar Radda, yace ya shiga tseren takarar gwamna ne a matsayin sadaukarwa don gyara jihar.
A cewar tsohon shugaban hukumar SMEDAN, lashe tikitin takarar gwamnan Katsina a inuwar APC ya ƙara fayyace masa ƙalubalen dake tattare da siyasar Najeriya.
Dikko yace a shirye yake ya yi sadaukarwan da ake bukata domin ɗaga darajar Katsina ta zama abin koyi ga sauran jihohin faɗin Najeriya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ɗan takarar jam'iyyar APC ya yi wannan furuci ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a babban birnin jihar Katsina ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dikko ya bayyana cewa akwai buƙatar 'yan siyasa a Najeriya su gaggauta canza tunanin azurta kansu su koma ga sadaukarwa don inganta rayuwar al'ummar ƙasa.
Dr. Dikko yace:
"Ina son siyasa, da farko na ɗauƙa shagalin shan shayi ne amma da aka zaɓe ni a matsayin ɗan takarar APC komai ya canza, ina da nauye-nauye da yawa a nan (ya nuna kansa da yatsa)."
"Na san cewa nauyi zai ƙara mun yawa idan na lashe zaɓe, saboda haka siyasa sadaukarwa ce kuma a shirye muke mu sadaukar kan mutanen mu saboda dole mu yi, idan bamu yi ba, wani gurɓatacce zai karbi ragama ya ƙara dagula lamarin."
"Allah ya san niyyata, na zo ne na ba da tawa gudummuwar, na sadaukar da rayuwata da komai nawa a wannan turba. Idan Allah yasa muka kai ga gaci, zamu gode masa, idan akasin haka ne ma zamu gode masa."
"Allah ne kaɗai ke ba da mulki ga wani ko ya ɗauke," Inji Dikko Umar Radda.
Akwai abubuwan da za'a canza sosai a siyasar Najeriya - Dikko
Dakta Dikko wanda ya nuna damuwarsa kan tsarin siyasar Najeriya yace akwai aiki tuƙuru a gaba matukar ana son komai ya koma kan hanya mai kyau.
"Siyasa a ƙasar nan ba ta kai ko ina ba, ba ta kan aƙida ko sadaukarwa, cigaban mutane masu ƙaramin karfi, siyasa ake ta handama ta ni kuma ni kaɗai da kaina, wannan ita ce gaskiya, kashi 95% na yan siyasa don kansu suke yi."
"Zasu ce maka domin talakawa suke yi amma ƙarya ce ba domin mutane suke yi ba. Ba'a tallafa wa mutanen da ke ƙasa."
A wani labarin kuma Gwamna Fayemi Na Jihar Ekiti Ya Rushe Majalisar Zaratarwan Gwamnatinsa
Wannan matakin na zuwa ne yayin da ake shirin rantsar da sabon zaɓaɓɓen gwamna mai jiran gado, Biodun Oyebanji.
A ranar 16 ga watan Oktoba, 2022 gwamna Fayemi zai miƙa ragamar mulki hannun sabuwar gwamnati da mutane suka zaɓa.
Asali: Legit.ng