2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

  • Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na APC, ba zai samu sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2023 ba
  • Hakan ya faru ne sakamakon tafiyar da Tinubu yayi zuwa Birtaniya domin ganawa da wasu kungiyoyi
  • Kashim Shettima, abokin takararsa ne zai samu zuwa taron wanda tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ke jagoranta

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ba zai samu damar saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2023 ba.

Tinubu, wanda a yanzu haka yana kasar Birtaniya, ba zai samu halartar taron saka hannu kan yarjejeniyar da kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ya shirya ba,wanda shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ke shugabanta.

Tinubu da Shettima
2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abokin takararsa Sanata Kasim Shettima ne zai wakilce shi a wurin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fara kamfen zaben 2023, jigon APC ya ce bai san inda Tinubu yake ba

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Premium Times ta rahoto cewa, Tinubu ya bar Najeriya a ranar Lahadin da ta wuce inda ya gana da wasu kungiyoyi a kasar Birtaniya. Sai dai akwai hasashe cewa ya je neman magani ne kasar.

Bayan tafiyarsa, kwamitin yakin neman zabensa ya dage kaddamar da kamfen dinsa har sai baba ta gani. Kwamitin ya sanar da cewa za a fadada sunayen ne domin samun biyan bukatun jam’iyyar.

An gano cewa, mambobi 422 na PCC da Sakataren Majalisar, James Falake ya saki, bai yi wa gwamnonin dadi ba, inda suka yi barazanar janye goyon bayansu ga yakin neman zaben.

A ranar Laraba ne aka fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya bisa jadawalin INEC yayin da 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba ya kasar nan.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku Zai Bi Wajen Maganin Akidar Biyafara Da Tayi Shekara da Shekaru

An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

A wani labari na daban, manyan alamu na nuna cewa mai 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya shuka sabuwar rigima a kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa (PCC) bayan ya zagaye shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugabancin jam'iyya da gwamnonin jam'iyyar wurin kafa kwamitin.

Jaridar Thisday ta rahoto cewa, sassa uku ne aka tsara wanda ya hada da 'dan takarar shugaban kasa, jam'iyya da shugaban kasa wadanda zasu samu jagorancin gwamnoni tunda su ne zasu jagoranci yakn nemen zaben a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng