2023: Jerin Sunayen Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Da Suka Kaurace Wa Kaddamar da Tawagar Kanfen Atiku
- Gwamnonin biyar ciki har da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, da wasu ƙusoshin PDP ba su halarci taron buɗe kamfen ɗin Atiku ba
- Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da wani tsohon ministan duk ba'a gansu a wurin taron ba wanda ya gudana a Abuja
- Ana ganin haka ta faru ne sakamakon rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar PDP tun bayan kammala zaɓen fidda gwani
Babbar Jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a yau Laraba 28 ga watan Satumba, 2022 a birnin tarayya Abuja domin tunkarar zaɓen 2023.
Amma wasu jiga-jigan jam'iyyar sun ƙauracewa taron inda aka neme su aka rasa a cibiyar taron ƙasa da ƙasa (ICC) dake Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Jerin sunayen waɗanda ba su halarta ba
Legit.ng Hausa ta tattara muku sunayen gwamnoni da wasu jiga-jigai da ba'a gani a wurin taron ba, sune kamar haka:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.
2. Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.
3. Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
4. Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.
5. Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya.
6. Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
7. Tsohon ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Farfesa Jerry Gana.
Sunayen waɗanda suka halarci taron
1. Gwamna Bala Muhammed na Bauchi
2. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sakkwato
3. Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta
4. Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom
5. Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa
6. Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo
7. Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
2023: Jonathan, Wike da Wasu Kusoshin PDP Ba Su Halarci Taron Kaddamar da Litattafai da Kamfen Atiku Ba
8. David Mark
9. Abubakar Bukola Saraki
10. Anyim Pius Anyim
11. Shugaban BoT na ƙasa, Sanata Adolphus Wabara
12. Ghali Na'abba
13. Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Ndidi Elumelu
14. Mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Damagun
15. Tsohon shugaban PDP, Prince Uche Secondus
16. Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo.
A wani labarin kuma Wani Gwamnan PDP Ya Yi Watsi Da Atiku Abubakar Yayin Da Ya Kai Ziyara Kudu Maso Gabas
Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya yi watsi da zuwan Atiku yankin kudu maso gabas, bai halarci wurin taron ba.
Mai neman shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya kai ziyara Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsakin jam'iyya na yankin.
Asali: Legit.ng